Monday, February 23
Shadow

Duk Labarai

Dalilin da yasa na koma Jam’iyyar APC>>Shehu Sani

Dalilin da yasa na koma Jam’iyyar APC>>Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa ya koma Jam'iyyar APC. Sanata Sani ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV. Yace Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ne ya jawoshi ya koma Jam'iyyar ta APC. Yace dama can yana daga cikin wadanda suka kafa jami'iyyar a Kaduna har aka ci zabe. Yace sun samu rashin jituwa da Gwamna El-Rufai ne a wancan lokacin shiyasa suka bar Jam'iyyar kuma yanzu Gwamna Uba sani ya dawo dasu.
Ashe ba yau aka fara ba: Yanda wata mata ta taba Fallawa Sanata Godswill Akpabio mari bisa zargin cewa ya bata makudan kudi dan ta amince yayi lalata da ita

Ashe ba yau aka fara ba: Yanda wata mata ta taba Fallawa Sanata Godswill Akpabio mari bisa zargin cewa ya bata makudan kudi dan ta amince yayi lalata da ita

Duk Labarai
A yayin da dambarwar sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio ke ci gaba da bayyana inda take zarginsa da cewa ya nemi yin lalata da ita. An koma baya a tarihi a lokacin Sanata Godswill Akpabio yana ministan Ma'aikatar harkokin Niger Delta, Tsohuwar shugabar riko ta hukumar raya yankin Niger Delta watau NDDC, Joy Nunieh ta zargeshi da cewa ya nemi yin lalata da ita. A wancan lokacin har fallaasa mari ta yi inda tace dalili shine ya bata kudi wai ta yadda yayi lalata da ita. Matar dai itama ta bayyana wannan zargi ne a gidan talabijin na Arise TV inda tace yana tunanin zai iya canja mata tunani da kudi? Tace itace mace ta farko data taba falla masa mari amma yaki gayawa mutane kuma tana zarginsa da neman yin lalata da ita. Saidai a wancan lokacin Akpabio yace bata da lafiya ...
An kama Fasto da yin mu’ujizar karya inda yace ya mayar da wata mata me kudi amma sai bayan kwanaki aka ganta tana sayar da Lemun Kwalba

An kama Fasto da yin mu’ujizar karya inda yace ya mayar da wata mata me kudi amma sai bayan kwanaki aka ganta tana sayar da Lemun Kwalba

Duk Labarai
Wani fasto me suna Ebuka Obi ya shiga idon Duniya bayan da aka kamashi yana yiwa mabiyansa karya ta hanyar mu'ujizar karya. Faston dai ya kai wata mata cocinsa me suna Zion Prayer Movement Outreach inda ta yi ikirarin cewa da tana da 300,000 amma data hadu da faston kudinta sun yi albarka har ta sayi gidan Miliyan 500 a Lekki jihar Legas. Saidai kwanaki bayan yin wannan ikirari, An ga matar tana sayar da lemun Kwalba. Matar dai har wani gida ta je ta nuna wanda tace nata ne amma daga baya me gidan sai da ya kamata akan ikirarin da ta yi na gidansa. A baya dai, Faston ya taba yin ikirarin warkar da marigayi dan fim din Kudu, John Okafor wanda aka fi sani da Mr. Ibu daga cutar dake damunsa amma kuma sai gashi daga baya dan fim din ya mutu. Faston dai na ikirarin cewa shi annab...
Kalli Bidiyo: Bill din NEPA yana cikin bashi da ake bin mutum idan ya mutum>>Inji Dr. Bashir Aliyu Al-Furqan

Kalli Bidiyo: Bill din NEPA yana cikin bashi da ake bin mutum idan ya mutum>>Inji Dr. Bashir Aliyu Al-Furqan

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Dr. Bashir Aliyu Al-Furqan ya bayyana cewa kudin wuta da ake bin mutum bashi yana cikin bashin da ake binsa wanda kuma ya kamata a biya masa. Malam ya bayyana hakane bayan da wasu suka aika masa Tambaya game da mahaifinsu da ya rasu inda suka ce ana binsa bashin kudin NEPA na Naira dubu dari 4. Malam yace tabbas ya kamata a biya dan kuwa wutar mutum saya yayi ba tasa bace ba dan haka ba da saidai ya sayi Diesel ko Fetur dan ganin haske. Malam yace ko da mutum yana tantamar kudin wutar da yake biya baya shan wutar, yace gara ya zamana kai ne kake bin bashi ba kaine ake bi ba. Kalli Bidiyon anan:
Kotu ta dakatar da JAMB hana dalibai masu shekaru kasa da 16 samun Admission a jami’o’i

Kotu ta dakatar da JAMB hana dalibai masu shekaru kasa da 16 samun Admission a jami’o’i

Duk Labarai
Babbar Kotun jihar Delta ta yi doka inda tace hana 'yan kasa da shekaru 16 samun gurbin karatu a jami'o'in Najeriya da hukumar JAMB ke yi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa. Karar wadda aka sakawa sunan John Aikpokpo-Martins v. Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) & four ohers ta kalubalanci JAMB kan hana 'yan kasa da shekaru 16 shiga jami'a. Mai shari'a, Hon. Justice Anthony O. Akpovi ya amince da bukatar masu kara inda yace hukumar JAMB ta sabawa ka'ida idan tace 'yan kasa da shekaru 16 ba zasu samu gurbin karatu a jami'o'in Najeriya ba. Da wannan hukunci, a yanzu kotun tace duka jami'o'i su rika daukar dalibai da suka cika sharudan dauka gurbin karatu ba tare da la'akari da shekarunsu ba. A ranar 16 October 2024 ne JAMB ta fito da sabuwar dokar hana 'yan kas...
An saci Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya ta hanyar amfani da BVN na Jabu

An saci Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya ta hanyar amfani da BVN na Jabu

Duk Labarai
Hukumar dake kula da warware sarkakiyar kasuwanci tsakanin bankunan Najeriya NIBSS ta bayyana cewa an yi amfani da BVN na karya aka sace Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya. Hukumar tace wasu gungun 'yan Damfara ne suka rika amfani da hotunan mutane hadda 'yan kasashen waje suna basu sunayen 'yan Najeriya suka bude BVN. Rahotan yace bayan an bude BVN din an yi amfani dashi aka bide accounts a bankuna daban-daban na kasarnan wanda dasu ne aka yi amfani aka yi damfarar. An dai kulle wasu daga cikin account din da aka yi amfani dasu wajan yin wannan damfarar sannan an kai rahoton wasu masu POS da aka yi amfani dasu wajan damfarar gurin jami'an tsaro.
Ba zamu iya hana mutane biyan kudin fansa da harajin da ‘yan Bìndìgà suke sawa mutane ba>>Sojoji suka magantu

Ba zamu iya hana mutane biyan kudin fansa da harajin da ‘yan Bìndìgà suke sawa mutane ba>>Sojoji suka magantu

Duk Labarai
Sojojin Najaria da suka yi ritaya sun bayyana cewa abune me wuya a iya hana mutanen kauyuka ci gaba da biyan 'yan Bindiga kudin fansar danginsu da aka kama ko kuka kudin Harajin da 'yan Bindiga suka kakaba musu. 'Yan Bindiga kan kakaba Haraji me yawa tsakanin Naira Miliyan 20 har zuwa naira Miliyan 200 ga kauyuka au tursasa mutane biya ko kuma su kai hari garin. A watan July na shekarar 2024, 'yan Bindiga sun kakabawa mutanen garin Toro dake jihar Benue harajin Naira Miliyan 20 inda kowane gida a kauyen sai da ya biya Naira Dubu 50 aka tattara kudin. Hakanan a watan Satumba na shekarar 2024 Bello Turji ya kakabawa garin Moriki na karamar hukumar Mulki ta Zurmi dake jihar Zamfara harajin Naira Miliyan 30. Hakanan a watan Janairu na wannan shekarar, 2025 da muke ciki akwai wani d...
Ki kiyayi kanki ki janye zargin da kikewa dan mu in ba haka ba wallahi zamu durkusa mu gayawa Allah ya mana maganinki>>Matan Inyamurai dana Niger Delta suka gargadi Sanata Natasha Akpoti

Ki kiyayi kanki ki janye zargin da kikewa dan mu in ba haka ba wallahi zamu durkusa mu gayawa Allah ya mana maganinki>>Matan Inyamurai dana Niger Delta suka gargadi Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Matan yankin Niger Delta dana jihohin Inyamurai sun hadu sun gudanar da zanga-zanga inda suke Allah wadai da tonon sililin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio. Matan sun bayyana cewa, su a yankinsu suna girmama mazansu dan haka ba zasu bari sanata Natasha Akpoti ta wulakanta dansu ba. Daya daga cikin matan me suna Mrs Grace Mathias da suka fito yin zanga-zangar a garin Uyo na jihar Akwa-Ibom ta gargadi sanata Natasha Akpoti cewa, ko dai ta janye wannan zargi da takewa Sanata Godswill Akpabio ko kuma su duka gwiwowi kasa su roki Allah ya sakko da bulalarsa ya zaneta. Matar tace wannan shine karo na karshe da zasu bari Natasha ta kara zargin dansu. Tace ba zau kyaleta ta cimma burinta na wulakanta dansu ba.
Lamari ya kara kazancewa tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio, Mijinta yace Akpabio abokinsa ne kuma yasan yana neman matarsa

Lamari ya kara kazancewa tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio, Mijinta yace Akpabio abokinsa ne kuma yasan yana neman matarsa

Duk Labarai
Lamari tsakanin Sanata Godswill Akpabio wanda shine kakakin majalisar dattijai da sanata Natasha Akpoti dake zarginsa da neman yin lalata da ita ya kara kazancewa. Mijin Natasha, High Chief Emmanuel Uduaghan ya bayyana cewa, yasan da maganar neman matarsa da sanata Godswill Akpabio ke yi. Yace asalima Sanata Godswill Akpabio abokinsa ne dan haka a matsayinsa na basarake kuma suna da alaka me karfi tsakaninsa da Sanata Godswill Akpabio bai nemeshi da fada ba, ya sameshi suka warware matsalar tsakaninsu inda ya mai alkawarin ya daina neman matarsa. Saidai, High Chief Emmanuel Uduaghan yace matarsa ta ci gaba da kawo mai korafin cewa, Sanata Godswill Akpabio ya ci gaba da neman yin lalata da ita. Dan hakane High Chief Emmanuel Uduaghan yake neman cewa a girmama matarsa wajan binci...
An yankewa malamin jami’a hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da yiwa dalibarsa Fyàdè

An yankewa malamin jami’a hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da yiwa dalibarsa Fyàdè

Duk Labarai
Wata kotun musamman dake kula da rikice-rikicen cikin gida dake Ikeja jihar Legas ta yankewa wani malami a kwalejin ilimi ta Adeniran Ogunsanya College of Educatio daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa dalibarsa fyade. Malamin me suna Kolawole Muyiwa ya musanta zargin da ake masa bayan da aka gurfanar dashi a gaban kotun. Ya aikata laifinne a ranar 11 ga wata October na shekarar 2021 a farfajiyar makarantar. An gabatar da shaidu da suka hada 'yansandan da suka yi bincike akan lamarin, da lauya da wadda akawa fyaden. Mai shari'a, Justice Rahman Oshodi ya bayyana cewa, duka wadanda suka bayar da shaida akan lamarin labarinsu yayi daidai da wadda akawa fyaden dan haka aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.