Matafiya na shan wuyar sayen tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna ta intanet
Duk da shigo da tsarin sayan tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta intanet da gwamnatin Najeriya ta yi a shekarar 2021, har yanzu fasinjoji na shan dan karen wuya kafin samun shi.
Tsohon ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi ne ya fito da tsarin a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, da nufin magance cuwa-cuwar saida tikitin da ake zargin ma'aikatan wurin na yi.
Gwamnatin Najeriya ta kashe naira miliyan 900 domin inganta hakan, sai dai bincike na baya-bayan nan da jaridar Solacebase ta fitar, ta raiwato a tashar jirgi ta Idu da Kubuwa a Abuja babban birnin kasar ya nuna bata sauya zani ba.
Dubban matafiyan da a kowacce rana suka dogara da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna na shan dan karen wuya kafin samun tikitin, ko dai dalilin rashinsa a intanet...








