Wani bawan Allah me suna Salihu Byezhe ya rasu ana tsaka da sallar Asuba tare dashi.
Lamarin ya farune a kauyen Gudaba dake Kuje a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin garin me suna Musa Dantani yace Salihu ya rasu ne a yayin da yake Sallar Asuba a masallacin garin.
Yace Salihu ya gama yin Sahur ya tafi masallaci, ana tsaka da sallah ya yanke jiki ya fadi, an garzaya dashi Asibitin Kuje inda acan Likita ya tabbatar da ya rasu.
An alakanta rasuwar tashi da hawan jini.
An yi jana'izarsa da misalin karfe 10:12 am kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false}
Wani dansanda dake aikin bayar da hannu a kan titin Akure jihar Ondo ya dauki hankula sosai bayan da aka ga yana aikin amma yana daukar kansa akan Tiktok Live.
https://www.youtube.com/watch?v=bXwPneb-YVU?si=NhW7QByz6kFKGsmM
Bayan ya bayar da hannu akan jishi yana cewa Taptap alamar masu kallo su aika masa da kyauta.
Kamfanin samar da wutar Lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa, ya samar da wutar lantarki me karfin 5,801 megawatts wanda a Tarihin Najeriya ba'a taba samun wutar lantarki me karfin hakan ba.
Saidai 'yan Najeriya dake amfani da wutar sun musanta wannan ikirari inda suka ce basu gani a kasa ba dan kuwa yankuna da yawa na kasar na kwana cikin duhu.
A ranar Alhamis ne dai shugaban hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja ya tabbatar da hakan.
Yace sun samu wannan nasara ne a ranar 4 ga watan Maris.
Yace kuma rassan kamfanin wutar na jihohi sun tura wutar gaba daya zuwa ga 'yan Najeriya.
Jami'an hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya sun gayyaci tsohuwar ministar matan ƙasar, Uju Kennedy-Ohanenye domin amsa tambayoyi.
Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce hukumar na zargin Ms Kennedy da karkatar da naira miliyan 138.4 cikin kuɗin da aka ware wa ma'aikatar a kasafin kuɗin 2023, da ɓarnatar da kuɗi da kuma saɓa ƙa'ida wajen wasu abubuwa.
Hukumar na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kuɗin domin amfanin kanta, ciki har da kuɗaɗen da aka ware domin shirin tallafa wa mata na P-BAT.
Tsohuwar ministan ta isa harabar hukumar da safiyar ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi, kuma bayanai na cewa har yanzu ana ci gaba da yi mata tambayoyin, kamar yadda kafofin ya da labaran ƙasar suka ruwaito.
Uju Kennedy-Ohanenye na ɗaya daga cikin ministoci biyar d...
Majalisar Wakilan Najeriya ta gabatar da wani ƙudirin da zai ƙwace wa hukumar zaɓen ƙasar ikonta na yi wa jam'iyyun siyasar ƙasar rajista da kula da ƙa'idojin jam'iyyun.
ƙudurin - wanda kakakin majalisar wakilan ƙasar Hon.Tajudeen Abbas tare da haɗin gwiwar Hon Marcus onobun daga jihar Edo suka gabatar - ya buƙaci a samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta kula da batun yi wa jam'iyyu rajista da kula da ƙa'idojinsu da ɗaukar nauyin jam'iyyun.
Tuni dai ƙudirin ya wuce karatu na biyu a zauren majalisar.
Haka kuma ƙudirin ya buƙaci da kafa kotu ta musamman don sauraron ƙorafe-ƙorafen jam'iyyu domin magance rigingimu tsakanin mambobin jam'iyyu.
Yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon. Onobun ya ce matakin ya zama wajibi, la'akari da yadda ake yawan samun rigingimun tsakanin jam'...
An sanar da mutuwar fitaccen ɗan siyasa Adedoyin Ajibike Okupe (22 ga watan Maris 1952 - 7 ga watan Maris 2025), wanda aka fi sani da Dr. Doyin Okupe da safiyar Juma'a.
Okupe likita ne kuma ɗan siyasa wanda ya kafa cibiyar kula da lafiya ta Royal Cross kuma ya kasance sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar National Republican Convention (NRC).
An taba tsare shi a ƙarƙashin mulkin marigayi Janar Sani Abacha, kuma daga baya aka hana shi shiga takarar fid da gwani a jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP). Daga baya, ya kasance ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun.
Okupe ya kasance mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai a gwamnatin Olusegun Obasanjo da kuma babban mataimaki na musamman kan harkokin jama'a ga Goodluck Jonathan.
Ya mutu ya bar mata ɗaya da ƴa...
Rahotanni daga legas na cewa, hukumar sojojin sama sun kai farmaki ofishin hukumar wuta ta jihar, Ikeja Electric inda suka ci zarafin ma'aikatan hukumar ciki hadda shugabar ma'aikatar.
Lamarin ya farune bayan da Hukumar sojin sama dake barikin Sam Ethan Base aka dauke musu wuta saboda kasa biyan bashin sa ake binsu.
https://www.tiktok.com/@emmax.media/video/7478644385446415638?_t=ZM-8uTjgNbH846&_r=1
Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta ya nuna yanda sojojin suka ci zarafin wasu ma'aikatan hukumar.
Shugabar ma'aikatar, Folake Soeten tace sun kamata sun kulleta a cikin but din mota a yayin cin zarafin.
Saidai hukumar sojin saman na kokarin cewa bata san wane sojoji ne suka je suka aikata wannan lamari ba.
https://www.tiktok.com/@emmax.media/video/747864...
Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, Rev. Daniel Okoh ya bayyana cewa, Musulmai da Kiristoci duk daya ne. Ya bayyana hakane a wajan shan ruwan da ya gudana a Abuja inda ya je shima aka yi buda baki dashi.
Shan ruwan ya farune a masallacin Al-Habibiyya inda aka ciyar da masu Azumi 2300. Shugaban na kan ya bayyana muhimmanci zaman lafiya da hadin kai.
Ya kara da cewa, wani zai yi tunanin me ya kawo shugaban CAN masallaci? Yace ya je masallacin ne kuma zai sake komawa.
Yace akwai muhummacin mu fahimci juna kuma a zauna lafiya
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Gwamnatinsa na kokarin ganin kowane gida a Najeriya ya samu wadataccen abinci me gina jiki.
Hakan ya fito ne daga Ministan Noma, Abubakar Kyari a yayin da yake kaddamar da shirin Noman Rani da rabon abincin watan Ramadana a jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kokarin samar da yanayi me kyau da kuma karfafa manoma dan su samar da amfani gona wadatacce da zai sa a samu wadatar abinci a kasarnan.
Yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da aiki da gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi dan ganin ta samar da ci gaba ta bangaren Noma.