Saturday, January 10
Shadow

Duk Labarai

Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024. Bidiyon faduwar shugaban ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna Tinubu a lokacin da yake yunkurin shiga motar faretin a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda ya rasa wani mataki wajen hawar motar ya faɗi. Tinubu mai shekaru 72, ya ce dimokraɗiyya ta cancanci faduwa. Da yake magana game da abin da ya faru a ranar Laraba, shugaban ya yi dariya da cewa "na rusuna ne don girmama dimokraɗiyya" a salon Yarbawa. Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da taron liyafar cin abincin na bikin dimokraɗiyya wajen kira ga hadin kan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko siyasa ba. Ya kuma jaddada cewa hadin kan Najeriya ba abu ne da za a iya yi...
Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Tsaro
Wasu ƴan bindiga sun kai wa wata tawagar sojoji da ke sintirin aikin sa ido kan bututun man fetur a garin Tibiri da ke yankin Dosso a kudu maso yammacin Nijar harin kwantan ɓauna inda suka kashe sojoji akalla shida. Rahoton wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara da cewa soja ɗaya ya ɓata sannan an lalata motoci biyu a harin. Rahoton bai bayyana ko an samu asarar rai a ɓangaren ƴan bindigar ba, ko kuma bayyana alakarsu da wasu ƙungiyoyi. Ƴan bindiga dai sun kasance suna gudanar da ayyukansu a wasu sassan Nijar da ke kan iyaka da arewa maso yammacin Najeriya. Har yanzu dai rundunar sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, al'amuran tsaron ƙasar Nijar ke ƙara taɓarɓarewa, inda a lokuta da dama ...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa na ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia. A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin. Rundunar sojin ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X. Cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙasa da ...
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Kaduna, Katsina
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi...
‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Jihar Zamfara, Tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar. Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu. Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar. A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence. “Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. " Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya b...
An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

Duk Labarai
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata. Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata. Jami'i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu. Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000...

Cin yaji ga mai ciki

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba. Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba. Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane. Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala. Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi. Dan haka kinfi kowa sanin kanki. Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki. Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka: Cin...
Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Duk Labarai
Jami'an 'yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8. Kwamishinan 'yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike. Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi. Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana'ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna. Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8. Kwamishinan 'yansandan yace za'a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.
Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky da Obi Cubana ta je ta kama 'yan siyasa masu sata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace idan da a yanzu gwamnati zata ce zata ciyar da mata kadai a Najeriya, saboda yunwar da ake ciki, maza da yawa zasu saka kayan mata su je karbar abincin. Bobrisky dai yana can daure a gidan yari saboda lika kudi a wajan biki yayin da shi kuma Obi Cubana aka gurfanar dashi ...
Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.