Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

Wata Sabuwa: Gwamnati ta saka haraji akan gawarwaki a Najeriya

Wata Sabuwa: Gwamnati ta saka haraji akan gawarwaki a Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Enugu ta sanar da saka haraji akan gawarwakin da aka ajiye a mutuwaren dake Asibitocin jihar. Saidai gwamnatin tace ba da niyyar tatsar mutane da tara kudade barkatai bane ta aikata hakan. Shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar, Mr Emmanuel Nnamani Ya yi karin haske kan lamarin inda yace duk gawar da aka kai mutuware a jihar kuma 'yan uwanta basu dauketa ba har ta wuce awanni 24 watau kwana daya to duk rana za'a rika biya mata harajin Naira 40 har zuwa ranar da za'a dauketa daga mutuwaren. Yace wannan ba sabuwar haraji bace kuma an dauki matakinne dan hana mutane kai gawarwakinsu mutuware a jihar.
Ji abinda Sanata Shehu Sani ya cewa matar tsohon gwamnan Kaduna, Hadiza El-Rufai bayan da ta masa gyaran kuskuren turancin da yayi

Ji abinda Sanata Shehu Sani ya cewa matar tsohon gwamnan Kaduna, Hadiza El-Rufai bayan da ta masa gyaran kuskuren turancin da yayi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Hadiza El-Rufai ta yiwa sanata Sanata Shehu Sani gyaran kuskuren Turancin da yayi a shafinsa na Twitter. Saidai da alama Sanata Sani bai ji dadin wannan gyara da ta masa ba inda mata martani da cewa, mun daina bibiyar juna a kafafen sada zumunta dan Allah ki kyaleni. https://twitter.com/ShehuSani/status/1845415955582640232?t=pDi22Zq04krnhwf4X1a_ew&s=19 Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda wasu ke cewa ya kamata ya karbi gyaran da aka masa wasu kuma na goyon bayansh...
Me neman kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa, Sunday Igboho ya kaiwa kasar Ingila bukatar ta goyi bayan kafa kasar Yarbawan

Me neman kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa, Sunday Igboho ya kaiwa kasar Ingila bukatar ta goyi bayan kafa kasar Yarbawan

Duk Labarai
Me fafutukar kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho ya kai takardar neman goyon bayan kafa kasar Yarbawan zuwa ga ofishin kasar Ingila dake Landan. Sunday Igboho yayi kokarin ganin kafa kasar ta Oduduwa amma bai cimma nasara ba inda a karshe sai da ya tsere daga Najeriya saboda yanda jami'an tsaro ke nemansa ruwa a jallo.
Kasar Namibia ta nemi Najeriya ta taimaka mata yin yaki da cin hanci

Kasar Namibia ta nemi Najeriya ta taimaka mata yin yaki da cin hanci

Duk Labarai
A kokarinta na yaki da rashawa da cin Hanci, Kasar Namibia ta nemi taimakon Najeriya wajan yaki da cin hanci inda tace tana neman shawarar Najeriyar ne saboda yanda kasar ke da kwarewa a fannin. Kasar ta Namibia ta samu ci gaba sosai saidai tana fama da matsalar rashawa da cin hanci wanda hakan yasa mutane basu da yadda da gwamnatin tasu. Kallon Nasarar da hukumomin yaki da rashawa da cin hanci na EFCC da ICPC ke samu yasa kasar ta Namibia ta nemi taimakon Najeriya wajan yaki da rashawa a kasarta. Kasar tana neman Najeriya ta taimaka mata wajan kafa nata hukukomin na yaki da rashawa da cin hanci.
Kalli Bidiyon wasu na rokon Kabarin Shehu ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur ya dauki hankula

Kalli Bidiyon wasu na rokon Kabarin Shehu ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur ya dauki hankula

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu mutane da suka kaiwa shehunsu ziyara sun rika rokonsa akan ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur da ake ciki. An ji suna gayawa shehun cewa, tsadar man fetur din ta hana ziyara. https://www.tiktok.com/@user2139247130913/video/7424490101805288710?_t=8qUdKfQU7O9&_r=1 Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta inda wasu ke kafurtasu wasu kuma na karesu.
Kalli Bidiyo: Me barkwanci na Kudu, Sabinus yayi wasa da addinin Musulunci kuma musulmai sun nuna masa fushinsu

Kalli Bidiyo: Me barkwanci na Kudu, Sabinus yayi wasa da addinin Musulunci kuma musulmai sun nuna masa fushinsu

Duk Labarai
Tauraron me barkwanci na kudu, Sabinus ya yi barkwanci da addinin Musulunci saidai musulmai da yawa aun gargadeshi. Yayi bidiyonne inda ya yi Atishawa sai wasu muryoyi ke ta magana a baya. https://www.tiktok.com/@sabinus1_/video/7400424002625211654?_t=8qUVFW0FfN8&_r=1 Da yawa dai sun bayyana masa cewa a addinin musulunci ba'a wasa da ibada.
Labari Me Dadi: Saboda karin kudin man fetur da NNPCL ta yi, Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta IPMAN tace zata shigo da mai me arha daga kasashen waje

Labari Me Dadi: Saboda karin kudin man fetur da NNPCL ta yi, Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta IPMAN tace zata shigo da mai me arha daga kasashen waje

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bayyana cewa, zata fara nemo man fetur me arha ko da daga kasashen wajene. Ta bayyana hakane ta bakin kakakinta, Chief Chinedu Ukadike a hirarsa da jaridar Vanguard. Yace a yanzu tunda NNPCL ba su ne kadai masu shigo da man fetur ba, zasu iya shigo da man fetur dinsu daga duk inda suke so. Hakan na zuwane bayan da kamfanin na man fetur na kasa, NNPCL ya kara farashin man fetur din zuwa Naira 998 a wasu guraren kuma Naira 1030 akan...
Masu baiwa Bola Ahmad Tinubu shawara ne ke saka mutane a wahala>>Inji Sanata Ali Ndume

Masu baiwa Bola Ahmad Tinubu shawara ne ke saka mutane a wahala>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa,Masu baiwa shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu shawara ne ke saka mutane a Wahala. Sanata Ndume ya baiwa shugaban kasar shawarar ya daina biyewa irin wadannan mutane dake son hadashi fada da 'yan Najeriya. Sanatan ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Ya kara da cewa, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana da kyakkawan fatan farantawa 'yan Najeriya rai amma masu bashi shawara ne matsalar. Yayi fatan cewa idan shugaban kasar ya dawo gida Najeriya zai duba wannan matsala ta tsadar rayuwa. Yace mutane basu da wadatar da zasu iya rayuwar wahalar da ake kakaba musu.
Mabarata sun kara yawa a Abuja

Mabarata sun kara yawa a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa mabarata dake yawo akan titi da jikin motoci dan samun abinda zasu ci sun kara yawa a babban birnin tarayya,Abuja. Hakan na faruwane duk da yake Abuja na da motoci na Alfarma da kuma gidaje na alfarma da sauransu. Hakanan hukumomi na kokarin dakile lamarin ta hanyar tallafawa mabaratan. Jaridar Daily Trust tace ta yi hira da wasu daga cikin mabaratan inda suka shaida mata cewa yawanci sun fito daga jihohin Arewa ne musamman wadanda ke fama da matsalolin tsaro. Mabaratan dai sun fito ne daga jijohin Niger, Zamfara, Katsina, Nasarawa, Kano, Adamawa, Borno da sauransu.
Ji sabon sunan tsokana da ake kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dashi wanda har Atiku Abubakar ma ya kirashi da sunan

Ji sabon sunan tsokana da ake kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dashi wanda har Atiku Abubakar ma ya kirashi da sunan

labaran tinubu ayau
A yayin da masu amfani da shafukan sada zumunta suka radawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sunan T-pain. Sunan dai ya watsu sosai inda har tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shima ya kirashi da sunan. https://twitter.com/atiku/status/1844369477690970492?t=yfNSmncXV6QvnpVcoUtYJw&s=19 T-pain dai shahararren mawaki ne a kasar Amurka amma 'yan Najeriya sun lakabawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shi. A sakon da ya fitar kan cire tallafin man fetur, Atiku Yace T-pain watau Tinubu be damu da wahalar da 'yan Najeriya ke ciki ba.