Bata gari sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari
Rahotanni daga kamfanin kula da wuta na kasa, TCN sun bayyana cewa, wasu bata gari sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari.
Rahoton yace an kaiwa Tangarahon wutar ne dake kan titin Ugwuaji zuwa Makurdi a jihar Benue hari.
Me kula da yada labarai ta kamfanin, Ndidi Mbah ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
Tace an yi barnar ne a ranar Asabar, 25 ga watan Janairu na shekarar 2025.
Tace da misalin karfe 3 na darene aka kai harin saidai mazauna garin sun ankara da maharan kamin su aikata wannan barna inda suka kai musu wawa, an kama mutum daya inda sauran suka tsere.
Sun mika wanda suka kama din ga 'yansanda kamar yanda Mbah ta bayyana.
Tace suna yabawa mutanen kauyen na Watuolo bisa wannan kokari inda ta yi kira ga sauran garuruwan da irin wad...








