Thursday, January 8
Shadow

Duk Labarai

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kano, Siyasa
Hukumar 'yansandan jihar Kano ta bayyana tsaka mai wuya da take ciki kan hukunce-hukuncen kotu har guda biyar da aka yi kan masarautar Kano. Kwamishinan 'yansandan jihar, Mr Usaini Gumel ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace sun tattara duka wadannan hukunce-hukuncen 5 sun aikewa da shugaban 'yansanda na kasa yayin da shi kuma ya aikawa da ministan shari'a. Yace suna jiran ministan shari'ar ya gaya musu da wane hukunci zasu yi amfani. Yace da zarar sun samu umarni daga ministan shari'ar, zasu zartas da hukuncin da doka ta amince dashi. Yayi kira kan kafafen yada labarai da su rika tantance labari kamin su yadashi.
An soki Peter Obi saboda kiran ‘yan Bindigar Arewa ‘yan Ta’dda amma yaki kiran ‘yan IPOB da ‘yan ta’adda

An soki Peter Obi saboda kiran ‘yan Bindigar Arewa ‘yan Ta’dda amma yaki kiran ‘yan IPOB da ‘yan ta’adda

Siyasa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya yi Allah wadai da harin da 'yan IPOB suka kai da ya kashe sojoji 5 a jihar Abia. A baya dai, an yi tsammanin ba zai yi magana akan lamarin ba saidai yazo yayi maganar. Amma kuma ya kaucewa kiran 'yan IPOB din da 'yan ta'adda. Tsohon hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan inda ya dauko wani tsohon sakon na Peter Obi wanda yayi magana akan wani hari da aka kai jihar Filato inda ya kira maharan da sunan 'yan ta'adda. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1796877604475040183?t=ynvg3_I3Mpo8KjuxyO6U9w&s=19 A zamanin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne dai aka ayyana kungiyar ta IPOB dake ikirarin kafa kasar Biafra da sunan kungiyar ta'ddanci.
An kama yaro dan shekaru 13, da dan shekaru 18 da wani me shekaru 45 da yin Fyade a jihar Gombe

An kama yaro dan shekaru 13, da dan shekaru 18 da wani me shekaru 45 da yin Fyade a jihar Gombe

Tsaro
Jami'an 'yansanda a jihar Gombe sun kama wani karamin yaro dan shekaru 13 saboda yiwa yarinya me shekaru 8 fyade. Ya aikata laifinne a karamar hukumar Akko dake jihar ta Gombe. Hakanan an kama wani Usman Husseini dan shekaru 18 da kuma wani Mohammed Yaya shi kuma dan shekaru 45 da duka ake zargi da yin fyade a jihar. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yaron ya ja yarinyar zuwa wata hanya da ba kowa inda acanne ya zakke mata. Shi kuma Mohammed Yahya yawa yarinya me shekaru 10 fyadene a lokuta daban-daban inda wani lokacin yake bata Naira 100 wani lokacin kuma ya bata Naira 50. Shima ya fito ne daga Tumu karamar hukumar Akko. Yace ana bincike akan lamuran kuma za'a gurfanar da wadanda ake zargi a Kotu.
An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

Tsaro
Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana sunayen sojoji 5 da ake zargin 'yan Kungiyar IPOB sun kashe. An kashe sojojinne a ranar Laraba a Obikabia dake jihar Abia. sunayen sojojin sune: • Sergeant Charles Ugochukwu (94NA/38/1467)• Sergeant Bala Abraham (03NA/53/1028)• Corporal Gideon Egwe(10NA/65/7085)• Corporal Ikpeama Ikechukwu (13NA/70/5483)• Corporal Augustine Emmanuel (13NA/70/6663) Hukumar sojojin Najeriya dai ta sha Alwashin daukar mataki me tsauri dan rama kisan sojojin nata.
‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

Tsaro
Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata. Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin. Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage. Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karat...
Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Tsaro
Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar. Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin. A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu. Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin. “Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji s...
An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema  wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

Tsaro
Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5. Wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton 'yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan. Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra. Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya. Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma'a yawanci yara basu je makaranta ba a garin. Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.