Kano: Za mu bijirewa dokar ta-ɓaci – Kwankwaso ya zargi gwamnatin Najeriya da haddasa rashin tsaro
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Ahmed Bola Tinubu da yiwa jami'an tsaron Kano zagon kasa sakamakon kin cire jami'an da ke gadin hambararren Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado. Bayero.
Kwankwaso ya kuma zargi Gwamnatin Tarayya da yunkurin haifar da wani sabon salo na kungiyar ta’addanci da masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya.
Kwankwaso dai na mayar da martani ne kan halin da ake ciki a Kano inda ake zargin hukumomin tsaron gwamnatin tarayya na goyon bayan hambararren Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa, Madobi, Sanata Kwankwaso ya ce al’ummar Kano za su bijirewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga gwam...








