Tuesday, July 7
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Duk Labarai
Ministan ci gaban Kiwo, Mukhtar Maiha ya gargadi 'yan Najeriya da su daina cin Ganda wadda ake yi da fatar dabbobi. Ministan yace akwai matsalar da cin gandar yakewa jikin dan adam. Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin samar da mayanka ta zamani wadda kowace sashe na jikin dabbar da aka yanka za'a iya fitar dashi cikin sauki ba tare da wahala ba. Ya kara da cewa, a jikin dabba babu abin yaddawa. Ya kara da cewa, a cikin kasafin kudin shekarar 2025 sun ware kudade masu yawa dan samar da gonaki da guraren kiwo na zamani
‘Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta a hanyar Sokoto zuwa Minna, 2 sun Mùtù wasu sun jikkata

‘Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta a hanyar Sokoto zuwa Minna, 2 sun Mùtù wasu sun jikkata

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Bindiga sun budewa motar matafiya kirar Sharon akan hanyar Sokoto zuwa Minna wuta i da suka kashe mutane biyu a cikin motar wasu kuma suka jikkata. Lamarin ya farune a yayin da motar ta doshi mabiyar 'yan Bindigar. Rahoton daga kafar Zagazola Makama ya bayyana cewa, wanda aka kashe din mace da namiji ne. An garzaya da gawarwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin IBB Specialist Hospital dake Minna.
Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Duk Labarai
An gano yanda wasu da ake zargin matsafane ke kwakule kaburbura bayan a binne a jihar Borno inda suke sace sassan jikin gawargwakin Lamari na kwanannan da aka gano shine wanda ya faru a makabartar Ramon Yashi dake Bayan Kwatas a cikin Birnin Maiduguri. An ga sabon kabari da aka binne amma an kwakuleshi an dauke gawar dake ciki, mazauna unguwar sun fara fargabar cewa da wuya idan babu matsafa ne suka aikata hakan ba. Wani shaida ya bayyanawa majiyarmu cewa, sun hango gawa na yawo akan ruwa, kuma sun je bakabarta suka iske an tone kabari babu gawar a ciki. Lamarin ya saka tashin hankali da fargaba a tsakanin mutanen dake zaune a kusa da makabartar inda suke kiran jami'an tsaro da gwamnatin jihar ta kai musu dauki.
Ya kamata a jinjinawa Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi>>Inji El-Rufai

Ya kamata a jinjinawa Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi>>Inji El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ya kamata a jinjinawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ya bayyana hakane a wajan gaisuwar marigayi, Edwin Clark a jihar Delta. El-Rufai yace yawanci mutane sun fi tunawa da abin ashsha da mutum ya aikata fiye da abin alkairi. El-Rufai yace hadda shi sun yi aiki a karkashin Atiku suka gyara tattalin arzikin kasarnan a lokacin amma ba'a magana akan lamarin ko dan basu yi rubutu akan lamarin bane?
Kin Rame da yawa: Anata cece-kuce akan sabbin hotunan Hadiza Gabon, ji ainahin dalilin da yasa ta rame

Kin Rame da yawa: Anata cece-kuce akan sabbin hotunan Hadiza Gabon, ji ainahin dalilin da yasa ta rame

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu hotunan tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon da suka bayyana a kafafen sadarwa sun jawo cece-kuce saboda yanda aka ga ta rame a cikin hotunan. Hadiza dai an santa da kiba da kumari, amma a yanzu ta rame inda wasu ke rade-radin cewa maganin rage kiba ta sha, wasu kuwa na cewa, aiki taje aka mata ta dawo siririya. Wasu kuwa na alakanta hakan da rashin lafiya. Kai wasu ma cewa suke ba ita bace saboda ramar da ta yi. Hadiza dai bata amsa kowa ba kan batun.
Wata mata dake koyawa samari kwailaye yanda ake jima’i a zahiri ta hanyar yin lalata dasu ta bayyana, tace ita ba karuwa bace ita malamace

Wata mata dake koyawa samari kwailaye yanda ake jima’i a zahiri ta hanyar yin lalata dasu ta bayyana, tace ita ba karuwa bace ita malamace

Duk Labarai
Wata mata 'yar kasar Australia data shahara wajan koyawa samari masu kananan shekaru da basu san mace ba yanda ake jima'i ta ce a daina ce mata karuwa. Annie Knight ta sha Alwashin budewa samari 500 ido ta hanyar kwanciya dasu da koya musu yanda ake jima'i da mace. Tace abinda take yi shine tana koyawa samarin yanda ake gamsar da mace ne da kuma girmama mace da kuma abinda bai kamata a yi ba. Tace mutane su daina zaginta saboda duk mazan da take koyawa jima'in sai sun yadda, ba fyade take musu ba. Matar me shekaru 28 ta bayyana cewa amma a yanzu tana neman mijin aure, saidai dole duk wanda zai aure ta ya amince ta ci gaba da rayuwarta ta koyawa samari yanda ake jima'i. Ta yi ikirarin cewa a shekarar 2024 ta koyar da maza 600 yanda ake jima'i.
Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan Hakar ma’adanai saboda matsalar tsaro

Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan Hakar ma’adanai saboda matsalar tsaro

Duk Labarai
Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan hakar ma'adanai saboda magance matsalar tsaro dake karuwa a jihar. Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ne ya bayyana hakan a wata sabuwar doka da ya sakawa hannu. Yace wannan mataki ya zama dole saboda yanda ake samun karuwar matsalar tsaro a jihar da suka hada da garkuwa da mutane da sayar da kwayoyi da shigowar 'yan kasar waje da sauransu. Ya bayyana cewa, dokar zata fara aiki ne ranar Juma'a 21 ga watan Janairu. Sannan yace daga yanzu sai wanda aka baiwa lasisin zasu rika hakar ma'adanai a jihar.
Hukumar ‘Yansandan Najeriya zata kammala jarabawar daukar ‘yansanda ta shekarar 2023

Hukumar ‘Yansandan Najeriya zata kammala jarabawar daukar ‘yansanda ta shekarar 2023

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya na shirin kammala jarabawar daukar sabbin 'yansandan da aka fara a tsakanin shekarun 2022/2023. Me magana da yawun hukumar ta PSC,Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manem labarai. Yace abu na gaba da za'a yi yanzu shine gwajin lafiyar wadanda za'a dauka aikin wanda zai fara daga February 26 zuwa March 12, 2025. Ya kara da cewa, wadanda suka yi jarabawar kwamfuta a ranekun 5th zuwa 6th March, 2024 amma sunayen su basu fito cikin wadanda suka yi nasara ba su sake zuwa shafin daukar aikin su duba ko sunayensu sun fito. Yace za'a yi gwajin lafiyar sabbin daukar aikinne a Asibitoci 17 Yace za'a bude shafinne a ranar February 22nd, 2025 da misalin karfe 12 na rana. Yace kuma duk wadanda aka gayyata zuwa wajan gwajin lafiy...