An saki DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 a gidan yari.
An saki Abba Kyari na tsawon sati biyu daga gidan yarin kuje dan ya sami yayi jana'aizar Mahaifiyarsa data rasu.
Kakakin gidan gyara hali na Abuja, NCoS, Adamu Duza ya tabbatar da sakin Abba Kyari.
Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin.
Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage.
Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karat...
Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin.
A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu.
Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin.
“Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji s...
Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5.
Wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton 'yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan.
Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra.
Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya.
Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma'a yawanci yara basu je makaranta ba a garin.
Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.
Sanata Dino Melaye ya ziyarci gidan wani abokinsa inda yaci karo da damisa.
Sanata Melaye ya bayyana mamakin abin saidai an gaya masa basa cutarwa.
https://www.youtube.com/watch?v=8PCMEVIwSRY
Ya saka bidiyon a shafinsa na sada zumunta inda yake bayyana mamakinsa.
Rahotanni na cewa an samu mutuwar mutane da dama sakamakon tsananin zafi a Indiya. Hukumomin jihohin gabashin ƙasar, Odisha da Bihar sun ce mutane 15 ne suka rasu a ranar Alhamis, kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin.
An haramtawa ma'aikata zirga-zirga a tsakiyar rana.
Ana hasashen cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a gabashi yayin da ake hasashen za a samu sauƙin zafin a Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar Indiya.
Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma'a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin.
A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.
Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.
Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta....
Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi 'yan ƙasar a kan fifita siyasar kuɗi maimaikon zaɓar mutane masu aƙidar da za su iya kawo canji.
Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu koma-baya saboda wasu 'yan siyasa da kan sayi ƙuri'un mutane ta hanyar ba su atamfa ko taliya.
A cewarsa, irin wannan tunani na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa al'ummar ƙasar cikin halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaron da hukumomi suka gaza shawo kansu ya zuwa yanzu.
Ya kuma ce rashin iya mulki ne ya haddasa taɓarɓarewar al'amura kamar tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya.
Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana haka a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasar Nijeriya a wani ɓangare na cika shekara 25 da mulkin dimokraɗiyya karon...