DA DUMI DUMINSA; Za’a ƙirƙiri Sabbin Jahohi guda 31, Mun samu bukatar ƙirƙiro sabbin Jihohi 31 a Najeriya – Kalu
Kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na Majalisar wakilan Najeriya, ya ce ya karbi buƙatar ƙirƙiro jihohi 31 daga sasan kasar, domin ƙara yawan jihohin da ake da su akan 36 dake wanzuwa yanzu haka. Shugaban kwamitin Benjamin Kalu, wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar wakilai, ya bayyana haka a zaman majalisar.Kalu ya ce bukatun sun hada da 6 daga Arewa ta Tsakiya, 4 daga Arewa ta Gabas, 5 daga Arewa ta Yamma, sai kuma 5 daga Kudu maso Gabas da 4 daga Yankin Kudu maso Kudu da 7 daga Kudu maso Yamma.Ga jerin bukatun kamar yadda Kalu ya bayyana.
Jihar Okun daga Kogi
Jihar Okura daga Kogi
Jihar Confluence daga Kogi
Jihar Benue Ala daga Benue
Jihar Apa daga Benue
Jihar FCT daga FCT
Jihar Amana daga Adamawa
Jihar Katagum daga Bauchi
Jihar Savannah daga Borno
J...








