An gano wani gidan Alfarma a kasar Amurka da ake zargin Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya siya da kudaden sata
An gano wani gidan Alfarma na miliyoyin daloli da tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya saya a kasar Amurka.
Sambo Dasuki dai an kamashi bisa zargin cinye Biliyoyin kudade da aka ware dan yaki da kungiyar Boko Haram a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Sannan a wannan sabon bincike da ya bayyana an gano Dasuki yayi amfani da kudaden wajan sayen godajen Alfarma a biranen Los Angeles, California da kuma babbar unguwar masu kudi ta McLean, Virginia, dake babban birnin kasar Amurka, Washington, DC.
Wata kungiya dake bincike da kwarmaton yanda ake sace kudaden talakawa a kasar Afrika me suna (PPLAAF) ce ta gano lamarin.
Kungiyar tace wasu dake taimakawa Dasuki sayen gidajen alfarmar Robert da Mimie Oshodin sun karbi akalla Da...








