'Yar gidan Jarumin Finafinan Hausa, Zainab Sharif Aminu Ahlan Ta Yi Saukar Kur’ani.
Wani abin burgewa shine, 'ya'yansa sa uku duk sun yi saukar Kur’ani.
Shi Ma Sanata Barau Jibrin Zai Aurar Da 'Yarsa A Fadar Sarki Aminu Ado Bayero, Kamar Yadda Kwankwaso Ya Aurar Da 'Yarsa A Fadar Sarki Sanusi II
Me za ku ce?
Sarauniyar kyau ta Najeriya, Chidimma Adetshina ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar kyau ta Duniya da aka kammala a gasar Mexico.
Sarauniyar kyau ta Najeriya da ta kasar Denmark ne suka kai Karshen gasar bayan doke sauran matan da suka kara dasu.
Saidai a karshe, Sarauniyar kyau ta kasar Denmark CE ta lashe gasar inda ta Najeriya ta zo ta biyu.
Saidai duk da haka an bayyana Sarauniyar kyau ta Najeriya a matsayin gwarzuwa wadda ta nuna bajinta sosai a gasar.
Da Safiyar ranar Lahadi be aka kammala gasar wadda aka Dade ba'a yi me armashi da daukar hankali irinta ba.
Babban Fasto na cocin (RCCG), Fasto Adebayo ya bayyana cewa addu'o'in da suke da taimakon Allah ne yasa darajar Naira bata fadi ba aka rika sayen dalar Amirka daya akan Naira dubu 10 ba.
Tun bayan da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta cire tallafin dala ne farashin dalar yayi tashin gwauron zabi zuwa sama da Naira 1,600.
Hakan ya taimaka wajan hauhawar farashin kayan masarufi.
'Yansanda a jihar Kano sun kama masu laifi gida 82. An kamasu ne tsakanin Nov. 1 zuwa Nov. 14.
Wanda aka kama din ana zarginsu da aikata laifukan kwacen waya, garkuwa da mutane da safarar kwaya.
Kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a hedikwatar 'yansandan jihar dake Bompai Kano.
Ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne bayan wasu dabaru da suka fito dasu na kama masu laifi.
Yace sun kwace makaman Bindiga AK 47 guda daya da bindigu kirar gida guda 3 da adduna da wukake guda 30 sai miyagun gwayoyi da sauransu.
Ya bayar da tabbacin ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya a jihar da yaki da aikata miyagun laifuka.
Kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya musanta Rahotannin dake cewa ya daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje inda a yanzu yake sayen man daga matatar man fetur ta Dangote.
Labarai sun yadu dai cewa NNPCL tace ta daina shigowa da man fetur daga kasashen waje.
Saidai a sanarwar da kakakin NNPCL din Mr Femi Soneye ya fitar yace wannan rahoto ba gaskiya bane.
Yace suna dubawane su ga idan shigo da man fetur din daga kasar waje yafi sauki to daga wajen zasu siyo idan kuma sayenshi a gida yafi sauki to sai su siya a gida.
Yace lamarin labarin cewa sun daina shigo da man fetur ba gaskiya bane inda ya jawo hankalin 'yan jarida da su rika yin bincike kamin watsa labaransu.
A kasuwar canji ta gwamnati a ranar Alhamis, farashin Naira ya fadi inda aka sayi dalar Amurka akan Naira N1,650.20.
Hakan na zuwa ne a yayin da tsadar rayuwa ta addabi 'yan Najeriya.
Tashi da faduwar farashin dala na daya daga cikin abubuwan dake kawo hauhawa da faduwar darajar Naira.
Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn a matsayin kasafin kudin shekarar 2025.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis bayan zaman majalisar zartaswa.
Yace nan da ranar Juma'a ko Litinin ake tunanin gabatarwa da majalisar tarayya da kasafin kudin a hukumance.