Tuesday, January 14
Shadow

Siyasa

Kotu ta samu Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa

Kotu ta samu Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa

Siyasa
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya zamo shugaban Amurka na farko da za a yankewa hukunci a kan tuhuma ta mugun laifi, bayan da masu taimaka wa alkali yanke hukunci suka same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 da ake yi masa. Dukkan tuhume-tuhumen na da alaka da karyar da ya yi a harkokin kasuwancinsa domin boye kudin da ya bayar na toshiyar baki a kan alakarsu da mai fitowa a fina-finan batsa wato Stormy Daniels a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasar a 2016. Da yake Magana a wajen kotun da ke Manhattan bayan samunsa da laifi, Donald Trump, wanda za a yankewa hukunci a watan Yuli mai zuwa, ya kira sakamakon zaman da aka yi a matsayin an yi masa almundahana da coge kuma hakan wani babban aibune. Sannan ya kara da cewa al’umma za su yanke hukunci na gaskiya a ranar za...
Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata. Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar dattawan Arewa ta ACF da yammacin ranar Alhamis. Yace zai ci gaba da yin aiki iya kokarinsa dan ci gaban Najeriya. Ya bayyana cewa, yana godewa 'yan majalisar zartaswarsa kan kokarin da suke amma zai rika dubawa yana tankade da rairaya dan gano wanda basa aiki yanda ya kamata dan canjasu.
A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

Siyasa
Shugaban kasar Kenya, William Ruto yace ba zai iya daukar hayar jirgin sama akan kudi dala Miliyan 150 ba ya dauki tawagarsa zuwa taro a kasar Amurka ba. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a kasarsa. Ya bayyana muhimmancin yin tattalin kudin talakawa inda yace kuma ya kamata shi ya fara nuna alamar abinda yake kira akai, watau rashin almubazzaranci. A baya dai, shima shugaban kasar Kenyan an zargeshi da yin wadaka da kudin talakawa.
A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Siyasa
Shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa 'yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri. Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki. Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.
YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Siyasa
YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe. Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Shugaban ya ce yana bakin ƙoƙarinsa a matakin tarayya amma ya kamata a sanya ido kan Gwamnoni su ma su riƙa yin abunda ya dace, su taimaki talakawa, "A lokacin zaɓe ana bin mutane lungu-lungu, gida-gida don neman ƙuri'unsu amma da zaran anci zabe sai kaga Gwamna ko dan siyasa ya tare a Abuja ya mance da talakawansa" inji Tinubu. Me zaku ce?
Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar kwadago, NLC ta dawo a ci gaba da tattaunawa game da mafi karancin Albashi

Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar kwadago, NLC ta dawo a ci gaba da tattaunawa game da mafi karancin Albashi

Siyasa
A jiya Laraba, wasu majiyoyi sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar Kwadago ta dawo a ci gaba da tattaunawa kan maganar mafi karancin Albashi. A zama na karshe dai an tashi baram-baram bayan da NLC din taki amincewa da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi. Hakanan wata majiyar tace kungiyar kwadagon ta amince da cewa zata amsa gayyatar ta gwamnati. Kungiyar dai ta baiwa Gwamnati nan da karshen watan Mayu da muke ciki a gama maganar mafi karancin Albashin ko kuma ta tafi yajin aiki.
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:

YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:

Siyasa
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan: Wanda ya rubuta - Lilian Jean Williams (1960) wanda yayi kidansa - Franca Benda Ga Sabon Taken National Anthem din Nigeria ⤵️ Nigeria, we hail thee,Our own dear native land,Though tribe and tongue may differ,In brotherhood, we stand,Nigerians all, and proud to serveOur sovereign Motherland. Our flag shall be a symbolThat truth and justice reign,In peace or battle honour’d,And this we count as gain,To hand on to our childrenA banner without stain. O God of all creation,Grant this our one request,Help us to build a nationWhere no man is oppressed,And so with peace and plentyNigeria may be blessed. Ku bayyana mana ra'ayinku kan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka na canja taken Najeriya....