Daga Yanzu Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Yi Wa Kowa Nadi, Cewar Gwamnatin Sokoto
Hakan dai ya biyo bayan wata sabuwar doka da majalisar dokokin jihar ta samar.
Me za ku ce?
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.
Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu
Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Tsohan Gwamnan Jihar Borno, Hajia Aisa Modu Shariff Rasuwa A Wata Asibiti Dake Abuja, Yau Lahadi Tana Da Shekara 93 A Duniya.
Za'a Yi Jana'izarta Gobe Litinin Bayan Kammala Sallar Azahar A Gidan Marigayi Galadima Modu Shariff Dake Kan Hanyar Damboa, Maiduguri Jihar Borno.
Allah Ya Jikanta Da Rahama!
Daga Jamilu Dabawa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki.
Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana.
Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake.
Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.
Zuwa Yanzu Alu'mma Da Dama A Jihar Kano Sun Yi Nadamar Zaɓen Jam'iyyar NNPP, Cewar Ganduje.
Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin karbe mulkin jihar Kano da Zamfara a zaben 2027, bisa yadda gwamnonin suke tafiyar da mulkin su.
Me za ku ce ?
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Cire harajin ya shafi kayan asibiti da suka haɗa da magunguna na ƙwayoyi da na ruwa, sirinji da allurai, sanke na rigakafin cizon sauro, abubuwan gwaji na gaggawa, da sauran kayan amfani a asibiti na yau da kullum.
Hakazalika, umarnin na shugaban ƙasa zai ƙara ƙarfafawa masana'antun sarrafa magunguna da kayan asibiti na cikin gida wajen kara inganta su da samar da su a wadace.
Wannan zai rage farashin magunguna da kuma wadatar su a lunguna da saƙon kasar nan don amfanin ƴan Najeriya.
Uwargidan tsohon shugaban kasa, Dame Patience Jonathan ta ce idan aka bukaci ta koma fadar shugaban kasa ta yi aiki a matsayin uwargidan shugaban Najeriya, za ta ki ba zata jeba.
A cikin wani faifan bidiyo na Misis Patience, wacce ta yi magana a ranar Juma'a a wurin wani taron jama'a, ta ce " damuwar Najeriya ta yi yawa", tana mai jaddada cewa ta yi kasa da lokacin da take kan mulki.
A cewarta, “Idan kun kira ni yanzu don naje villa, ba zan je wurin ba. Ba zan yi ba. Ba ku ga yadda nake matashiya ba? Damuwar tana da yawa.
“Matsalar Najeriya ta yi yawa. Idan Allah Ya yi nasarar fitar da ku daga cikinta, to ku tsarkake Shi. Ya kai ka can sau ɗaya, me yasa kake son komawa can kuma”?
Dimokuradiyya ta rahoto cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fice daga fadar shugaban ka...
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.
Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.
Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa'i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.
Lauyan El-Rufa'i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Sabod...
An ga wani hoto dake nuna sojojin kasar Yahudawan Israela suna taka tutar kasar Saudiyya me dauke da kalmar shahada.
Lamarin ya jawo tayar da jijiyoyin wuya matuka inda da dama suka ce dama addinin musulunci ne kasar Israelan take yaka ba kasar Palasdinawa ba kadai.
Wasu dai na zargin kasar Saudiyya da kin daukar matakan da suka dace dan baiwa palasdinawa kariya daga kisan da kasar Israela take musu.
Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da rahoton cewa, ƴan Najeriya sun koma cin bashi daga bankuna da manhajojin karɓar bashi saboda tsananin tsadar rayuwa domin samun biyan buƙata.
CBN ya ce an samu ƙaruwar masu ciyo bashi da kashi 12 cikin 100, inda ya kai kusan tiriliyan ₦3.9 a watan Janairun 2024.
An danganta wannan ƙaruwar ciyo bashin da hauhawar farashin kayan masarufi.
Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ruwaito cewa hauhawar farashin kaya ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu.
Hakan ya sa babban bankin ƙasar ya ƙara yawan kuɗin ruwa a jere zuwa kashi 26.25 bisa 100.
Hauhawar farashin kaya ya jefa ƴan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya ƙara tsadar rayuwa.
Wani bincike da SBM Intelligence ya gudanar ya nuna cewa k...