Sunday, July 21
Shadow

El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin Kaduna a kotu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.

Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.

Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa’i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.

Lauyan El-Rufa’i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Saboda haka El-Rufa’i ya buƙaci kotun ta ayya rahoton kwamitin majalisar dokokin jihar kan binciken ayyukan gwamnatinsa a matsayin haramtacce, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulki na jin ta-bakin wanda ake zargi.

Dama dai tsohon gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin, inda ya bayyana shi a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.

Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna “da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi”.

“[El-Rufai] ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna…ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.”

A farkon watan Yuni ne wani kwamiti da majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa ya gabatar da rahotonsa.

Lokacin da ya gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa’i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa’ida wajen cin bashin ba.

Wasu daga cikin laifukan da rahoton ya ce ya bankaɗo game da gwamnatin El-Rufa’i su ne:

 • Tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayu 2023, shugaban ɓangaren zartarwa na jihar Kaduna ya karya ƙa’idojin aikin ofishinsa kamar yadda suke a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.
 • Jefa jihar cikin ƙangin bashi na cikin gida da waje ta hanyar ha’inci ba tare da dalili ba, waɗanda suka zarce jimillar ɗaukacin basukan da jihar Kaduna ta taɓa ci daga shekarar 1965 zuwa 1999, kuma yawanci an karɓo bashin ne ba tare da bin ƙa’ida ba.
 • Bayar da kwangiloli barkatai ba tare da bin ƙa’ida ba kuma ba tare da bin diddigin aiwatarwa ba, wanda hakan ya haifar da yin watsi da kwangiloli da dama duk kuwa da kuɗaɗen da aka biya.
 • Bayar da izinin cire maƙudadan kuɗaɗen naira da dalar Amurka ba tare da bayanin yadda aka yi amfani da su ba, wanda hakan ya hana jihar samun isassun kuɗaɗen da za ta aiwatar da ayyukan ci gaba.
 • Haɗa baki da kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnati domin ha’intar gwamnati ta hanyar umurtar hukumar KADPPA ta biya ƴan kwangila kuɗi ba tare da bin ƙa’ida ba, kamar yadda yake ƙunshe a wata wasiƙa mai kwanan wata 21st Yuni, 2021.
 • Karkatar da kuɗi da halasta kuɗaɗen haram wanda ya saɓa da dokoki da ƙa’idoji, kuma ya kamata a miƙa shi ga hukumomin tsaro domin gudanar da zuzzurfan bincike tare da ɗaukar matakan da suka kamata.
Karanta Wannan  HOTUNA: Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da sauran manyan jami'an gwamnati yayin gabatar da sallar Juma'a yau a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Matakan da majalisar dokokin Kaduna ke son a ɗauka

Kwamitin na Majalisar dokokin jihar Kaduna ya ce: ya haƙiƙance cewa hujjoji sun bankaɗo ayyukan rashawa da dama a wajen tafiyar da lamurran gwamnati, da ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnatin jihar Kaduna tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023, kuma kwamitin ya bayar da shawarwari kamar haka:

 • Hukumar tara kuɗaɗen haraji ta jihar Kaduna ta cire kuɗi kuɗin da aka tara na cikin gida naira biliyan 20 waɗanda aka ajiye a wani asusun bankin Zenith, tare da umurtar bankin da ya mayar da duk wasu kuɗaɗe da ya cire waɗanda suka samo asali daga waɗannan kuɗade da aka ajiye.
 • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi na jihar daga watan 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tabbatar da tsaro na ƙasa domin fuskantar bincike.
 • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin babban akanta na jihar daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike
 • A tura duk waɗanda suka shugabanci hukumar tara kuɗaɗen haraji na jihar Kaduna daga 29 ga watan Mayu, 2015 zuwa 29 ga watan Mayu, 2023 ga hukumomin tabbatar da tsaro domin fuskantar bincike.
 • Kwamishinan kuɗi na jihar Kaduna da ke kan muƙami a yanzu ya sauka daga muƙaminsa domin samun damar gudanar da bincike yadda ya kamata kan ayyukan ma’aikatar kuɗin jihar daga 29 Mayu, 2015 zuwa 29 Mayu, 2023.
 • Shugaban hukumar bayar da ilimi a matakin farko mai ci a yanzu ya sauka domin bayar dadamar a binciki ma’aikatarsa kan ayyukan da ta gudanar daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
 • Shugaban hukumar fansho ta jihar Kaduna mai ci a yanzu ya sauka daga muƙaminsa domin samun gudanar da bincike yadda ya kamata kan ayyukan hukumarsa daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.
 • A tura duk waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban hukumar bunƙasawa da gudanar da kasuwannin jihar Kaduna daga 29 ga watan Mayun 2025 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike kan yadda suka tafiyar da ma’aikatar.
 • A tura shugaban shirin noman rani na alkama a Ruwan Sanyi da ke ƙaramar hukumar Kubau a shekarar 2016 ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike.
 • A tura tsohuwar shugabar hukumar KAPSO, Ms Dolapo Popoola zuwa wurin jami’an tsaro domin fuskantar bincike da kuma ƙwato kadadrorin gwamnati da ke hannunta.
 • A tura mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yaɗa labaru da sadarwa tsakanin watan Mayun 2025 zuwa watan Mayun 2023, Muyiwa Adekeye ga hukumomin tsaro domin fuskantar bincike kan hannunsa a kwangilolin gyara Hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna (KSMC).
 • A tura ɗaukacin shugabannin hukumar kula da tituna ta jihar Kaduna daga 11 ga watan Oktoba, 2017 zuwa Nuwamba, 2021 – in ban da Amina Ja’afar Ladan, wadda ta yi wata ɗaya kacal kan kujerar – zuwa ga hukumomin tsaro domin fuskantar zuzzurfan bincike kan yadda aka bayar da kwangiloli da kuma rashin ingancin ayyukan da aka bayar a lokacin shugabancinsu, sannan a sauya wa manyan jami’an hukumar wurin aiki zuwa wasu ma’aikatu da hukumomi masu alaƙa.
 • Dukkanin basuka na cikin gida ko na waje da gwamnatin jihar Kaduna ta karɓa tsakanin 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023, waɗanda kwamitin ya gano cewa ba a karɓe su kan ƙa’ida ba, babu ruwan gwamnati da su kuma daga yanzu ba za ta ci gaba da cika duk ƙa’idojin da suka ƙunsa ba.
 • Kwamitin ya lissafo sunan wasu kamfanoni waɗanda ya ce su mayar wa gwamnatin jihar Kaduna jimillar kuɗi biliyan 36,351,126,811.65 ko dai saboda an biya su kuɗi ba su yi aiki ba ko an yi aringizon kuɗi wajen biyan su ko kuma an karkatar da kuɗin.
 • A miƙa batun kuɗi naira biliyan 4,936,916,333.00 waɗanda kwamishinan kuɗi da babban akantan jihar suka cire ba tare da wata hujja ba tsakanin shekarun 2019 zuwa 2022 ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da ɗaukar mataki.
 • A miƙa batun kuɗi dalar Amurka miliyan 1.4 da aka cire daga asusun haɓɓaka tattalin arziƙin jihar tsakanin 30/10/2020 zuwa 06/05/2020 ga hukumomin tsaro domin gudanar da zuzzurfan bincike a kai.
Karanta Wannan  Hotuna: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Bakuncin Tsohon Ministan Yada Labaransa, Alhaji Lai Mohammed A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina Yau Lahadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *