Wednesday, January 15
Shadow

Tsaro

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Jihar Zamfara, Tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar. Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu. Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar. A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence. “Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. " Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya b...
2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin jami’anta da tsare tare da cin zarafin mata da yara da dama da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas. Mai magana da yawun rundunar Edward Buba ta bakin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Group Kaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa "ba za su damu da irin waɗannan kalamai na son kai da aka yi da niyyar rage kwarin gwiwar sojojin fafutuka don tabbatar da tsaro ba" Ya kara da cewa sojojin za su yi haɗin gwiwa mai inganci da Amnesty International idan akwai bukatar yin hakan kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ta'addanci da tabbatar da tsaro. Wannan martanin ya zo ne kwana guda bayan da Amnesty International ta zargi gwamnati da gazawa wajen bai wa ...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Katsina, Siyasa, Tsaro
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwamnati...
Wasu na shirin gudanar da zanga-zangar lalata Ranar Dimokuraɗiyya – DSS

Wasu na shirin gudanar da zanga-zangar lalata Ranar Dimokuraɗiyya – DSS

Tsaro
Rundunar 'yansadan Najeriya ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta ce ta samu labarin wasu na shirin fakewa da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar da zimmar aikata laifuka kuma ta nemi 'yan ƙasa su guji yin hakan. Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce an shirya zanga-zangar ne da gangan "domin ta dace da Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yuni". Ta alaƙanta zanga-zangar da gwagwarmayar neman ƙarin albashi mafi ƙaranci da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi, inda ta ce "gwamnatin tarayya ta fi son a warware matsalar cikin lumana har ma da maganar mafi ƙarancin albashi". "Sai dai kuma DSS na jaddada aniyarta ta kare ƙasar daga duk wani yunƙuri na wasu ƙungiyoyi na karya doka da oda. Sannan kuma za ta hada kai da sauran jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyi," in ji sanarwar. Ita ma runduna...
Hotuna: ‘Yan IPOB sun kashe ‘yansanda biyu a Imo

Hotuna: ‘Yan IPOB sun kashe ‘yansanda biyu a Imo

Tsaro
Rahotanni daga jihar Imo na cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan IPOB ne sun kashe 'yansanda 2 da kuma farar hula 1. Lamarin ya farune ranar Talata a Titin Oweri Ogikwe dake jihar. Hakanan dayan mutumin an harbeshine a cikin gida. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 6:25 na safe. Zuwa yanzu dai hukumar 'yansandan jihar batace uffan ba kan lamarin.
Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Katsina
Ƙungiyar gwamnonin kudu-maso-yammacin Najeriya sun nemi a kafa rundunonin ƴansanda mallakar jihohi. Sai dai kuma sun yi fatali da fafutukar da wasu ke yi na kafa ƙasar Yarabawa zalla. Wannan na cikin ajanda 11 da suka amince da su bayan taron da suka gudanar a Ikeja babban birnin jihar Legas a ranar Litinin. Gwamnonin sun kuma taɓo batun sabon mafi ƙarancin albashi, inda suka yi nuni da cewa zai zo da tsarin tarayya na gaskiya. Matsalar tsaro malace da daɗe tana ciwa jihohin ƙasar tuwo a kwarya, sai dai wasu na ganin kafa ƴansandan jihohin zai taimaka wajen magance matsalar. A baya dai rundunar ƴansandan ƙasar ta yi watsi da irin wannan buƙata ta kafa ƴnsandan jiha a ƙasar.
Ƴanbindiga sun kashe mutane 25 a Ƙanƙara jihar Katsina

Ƴanbindiga sun kashe mutane 25 a Ƙanƙara jihar Katsina

Katsina, Tsaro
Akalla mutane 25 aka hallaka, sannan aka sace wasu da dama a lokacin da ƴanbindiga suka kai hari a wani ƙauyen a jihar Katsina a arewacin Najeriya, a cewar hukumomi. Gwamman ƴanbindigar sun isa ƙauyen Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a ranar Lahadi da daddare ne, kamar yadda kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Babangida Mu'azu, ya shaida wa BBC Hausa. Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun dinga harbin kan mai uwa da wabi, yayin da suka fasa shaguna tare da sace mutanen da kawo yanzu ba a san adadinsu ba. Sai dai wasu rahotanni na cewa ƴanbindigar sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata kimanin wasu 30. A watan Disamba 2020, wasu ƴanbindiga sun sace ɗaliba 300 daga wata makarantar sakandare ta kwana ta maza da ke wajen Ƙankara, amma daga bisani aka sake su. Matsalar ƴanfa...
Gwamnatin jihar Plateau ta ɗage dokar hana yawo a Mangu

Gwamnatin jihar Plateau ta ɗage dokar hana yawo a Mangu

Tsaro
Gwamnatin jihar Filtao ta bayar da sanarwar dage dokar hana yawo da ta saka tun a watan Janairun wannan shekara a karamar hukumar mulki ta Mangu da kewaye. Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ne ya saka dokar hana fitan har na tsawon awa ashirin da hudu a kowace rana, bayan wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a kauyukan Punshit da Sabon-Gari inda suka kashe akalla mutum sha uku tare da jikkata karin wasu baya ga kona gidajen jama’a da dama. Gwamnatin Filaton ta bayyana cewa an saka dokar ne domin a samar da cikakken tsaro da zaman lafiya tsakanin kabilu daban-daban da ke fadin jihar.
Ji yanda sojan Najeriya da aka yi gar-ku-wa dashi ya kwace Bin-di-gar maharan ya kubutar da kanshi da sauran mutane

Ji yanda sojan Najeriya da aka yi gar-ku-wa dashi ya kwace Bin-di-gar maharan ya kubutar da kanshi da sauran mutane

Tsaro
Wani sojan Najeriya me mukamin Kyaftin yayi abin yabo inda ya kubutar da kansa da wansu sauran mutane da aka yi garkuwa dasu tare. Sojan me suna Captain J.O. Abalaka Ya kubutar da kansa ne a jihar Kogi bayan da aka yi garkuwa dashi. Lamarin ya farune makon da ya gabata a yayin da sojan ke kan hanyar zuwa Borno inda aka mayar dashi daga Jihar Rivers inda yake aiki. Sojan na cikin motarsa me kirar Toyota Corolla tare da karensa yayin da lamarin ya faru, saidai ya yi nasarar kwace bindigar AK47 daga hannun daya daga cikin 'yan Bindigar inda ya kori sauran. Sojan ya kuka kwace bindiga kirar hannu da sauran wasu abubuwa.