Friday, December 13
Shadow

Gombe

Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Gombe
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta sake kama wani matashi a jihar Gombe me suna Zachariyya Muhammad saboda yin likin kudin Naira a wajan wani biki. An kama shine ranar Asabar, 24 ga watan Mayu bayan ya lika kudin Naira dari 200 a wajan wani bikin G-Connect. Ko da aka nuna masa bidiyonsa yana likin, ya amsa cewa lallai shine, hukumar zata gurfanar dashi a gaban kotu. A baya dai EFCC ta kama mutane da yawa a jihar Gombe shima.