Tuesday, December 31
Shadow

Gyaran Gashi

Tsawon gashi cikin sati daya

Gyaran Gashi
Ana iya samun tsawon gashi cikin sati daya idan aka yi abinda ya dace kamar yanda zamu yi bayani a kasa: Hanya ta farko da ake iya kara gashi cikin sati daya itace ta amfani da man kwakwa, ko man Zaitun. Yanda ake yi shine, ana samun man kwakwa ko kan zaitun a dafashi, a sauke ya huce,amma kada a bari ya huce gaba daya, sai a taba da hannu a ji idan akwai dumi yayi daidai yanza za'a iya shafawa akai sai a rika dangwala ana shafawa akai, a shafa sosai ya shiga cikin gashi da kyau. A tabbatar an gauraye duka gashin dashi. A bari yayi mintuna akalla 30 sannan a wanke da shampoo. Hakanan masana sun kara da cewa, cin abinci me gina jiki da kyau da kuma motsa jiki da kuma murza gashin kai akai-akai watau a rika yi mai tausa har zuwa inda ya tsiro yana taimakawa kara yawan gashi sos...

Gyaran Gashi

Gyaran Gashi, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa na gyaran gashi wanda ba ma sai kin sayi mai ba idan kinso. A wannan rubutu, zamu kawo muku abubuwan gyara gashi daban-daban wanda za'a iya hadawa a gida: Man Zaitun: Ana samun man zaitun wanda ba'a hadashi da komai ba, a rika amfani dashi wajan gyaran gashi, man zaitun yana taimakawa sosai wajan kara yawan gashi, hanashi karyewa, sa gashi ya rika sheki da sauransu. Idan gashin kanki ya lalace, ko yana yawan bushewa ko yana kaikai, man zaitun na magance wadannan matsaloli. Ana shafa man zaitun akai, bayan mintuna 30 sai a wanke ko kuma idan anzo kwanciya sai a shafashi, da safe a wanke da ruwan dumi. Man Kwakwa: Bayan Man zaitun, ana kuma amfani da Man Kwakwa wanda ba'a gaurashi da komai ba wajan gyaran Gashi. Shima ana shafashi zuwa mintuna 30 sai a wa...