Zamu tafi Yajin aiki idan gwamnati bata mana karin albashi ba, Albashin da ake biyan mu yayi kadan>>Inji ASUU
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ta kasa karawa membobinta Albashi da kuma inganta jami'o'in Najeriya.
Wakilan kungiyar na jami'o'in Akwa-Ibom, Uyo, University of Cross River State, University of Calabar, da University of Uyo ne suka bayyana haka.
Sunce rabon da a duba albashinsu dan kari shekaru 15 kenan duk da cewa sauran bangarori na kasarnan an kara musu albashin a lokuta da dama.
Sun kuma ce akwai alkawuran kudade da gwamnati ta musu wanda har yanzu bata cika ba.
Kungiyar tace amma ana hakane gwammatin ta dauki Biliyan 90 ta baiwa mahajjata a matsayin tallafi.