Monday, January 13
Shadow

Amal Umar

Duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’>>Inji Amal Umar

Duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’>>Inji Amal Umar

Amal Umar
Jarumar fina-finan Kannywood, Amal Umar ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu mutane na yaɗa mummunar fahimtarsu game da halayen wasu jaruman shirya fina-finan. Amal Umar -wadda ta bayyana hakan cikin shirin Mahangar Zamani na BBCHausa - ta ce babban takaicinta shi ne yadda ake yi wa ƴan fim kallon marasa tarbiyya. Duk da cewa akwai labarai marasa daɗi da ake yaɗawa game da masu sana’ar fim, jarumar ta nesanta kanta daga dukkan zarge-zargen da al'umma ke yi wa 'yan fim. ‘’Kowa ba ya yi mana zaton alkahiri, sai dai ki ji ana karuwai ne su, ba su kwana a gidajensu, sun raina iyayensu, irin waɗannan abubuwan, amma ni na sani, kuma masu mu’amula da ni sun sani, duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’, in ji jarumar. Sauran baƙin da shir...