
Wannan wata matar aure ce a Arewa data dauki hankula bayan data bayar da labarin halin da mahaifiyarta ke ciki.
Tace Mahaifinsu ya rasu, dan hakane mahaifiyarta ta rika bin abokansa da ‘yan uwansa dan su taimaka mata ta rike yaran da ya bari.
Tace amma duk sai su rika bayyana mata cewa, sai ta bayar da kanta kamin su taimaka mata.
Tace suna hakane tun tana kin yadda har yanzu ta koma tana basu kanta suna bata abinda zata kula da yaran.
Tace ta gano hakane bayan da wata rana ta je gidan taga mahaifiyarta sai dare yayi take cin kwalliya ta fita
Tace ta fuskanci mahaifiyarta inda ta tambayeta ta fara bin mazane, tace mahaifiyar ta ta ce bata da yanda zata yi shiyasa, bata da jari dolece tasa take bin maza.
Tace dalili kenan da yasa ta shigo kafafen sada zumunta dan nemawa mahaifiyarta taimako.