Fârgaba Yayin Da Sarki Sanusi, Aminu Ado Bayero Suka Sanar Da Jagòrantar Sâllar Juma’a A Masallaci Ɗaya, Shin me zai faru?
DAGA: Abbas Yakubu Yaura
Tsòro ya mamaye tsòhon birnin Kano yayin da sarakunan biyu da ke hamayya da juna – Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka dawò dashi da Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige suka bayyana shirinsu na yin sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na fadar Sarkin.
Majiyar mu ta rawaito cêwa tuni mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke zaune a fadar, kuma kusa da Masallacin da ake fafatawa, ana sa ran zai jagoranci sallar Juma'a raka'a biyu.
Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagòranci Sallar Juma’a a babban masallacin fadar a matsayin sarkin birnin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Danburan Kanò, Munir Sanusi Bayero, ta bayyana matsayar Maimartaba Sarkin Kanò Muhammadu Sanusi II zuwa Masallacin...