Thursday, January 16
Shadow

Kano

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Duk Labarai, Kaduna, Kano
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin  Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna. Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter. Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar  Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna. Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.
Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Biyo bayan dambarwar data sarkake masarautar Kano, Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya fitar da sanarwa. Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun gidauniyarsa, ya bayyana cewa yana baiwa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Shawarar kada yayi abinda zai kawo hargitsi a jiharsa ta Kano. Malamin ya bayyana cewa, bai ji dadin abinda gwamnatin jihar Kano ta yi ba na sauke Aminu Ado Bayero ta nada Muhammad Sanusi II ba. Ya jawo hankalin gwamnatin jihar ta Kano cewa, ta yiwa doka biyayya dan zaman lafiya me dorewa a jihar ta kano. Shugaban gidauniyar ta Dahiru Bauchi, Ibrahim Dahiruin ya bayyana cewa, babu wanda yafi karfin doka. Yayi kira ga majalisar majalisar tarayya da ta yi doka da zata hana ‘yan siyasa amfani da damarsu wajan wulakanta sarakai ta hanyar saukesu. ...
DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu

DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu

Duk Labarai, Kano
DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu. Abin jira dai a gani shine ko ‘yansandan zasu bi umarnin Kotun, ganin cewa a baya ma an samu wata kotu ta bayar da umarnin hana sauke Aminu Ado Bayero amma umarnin bai yi amfani ba? Rigimar sarautar Kano dai ta dauki hankula sosai a kasarnan inda a karon farko aka samu sarakuna biyu a jihar da kowane ke cewa shine sarkin Kano.
WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu

WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu

Duk Labarai, Kano
WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu. Shi dai Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya zargi Nuhu Ribadu ne da baiwa tsigaggen sarkin Kano Aminu Ado Bayero jirgi biyu tare da jami’ań tsáro dan su banƙara a shígar da da shi masarautar Káno. Ya ce kuma Ganduje ne ya je wajań mai bawa shugaban kásar shawara kan harkar tsáro wato Nuhu Ribadu dómin aikata wannań mummunan aiki. A céwar mataimakin Gwamnan duk abinda za muyi zamuyi dan mu tabbatar haka bata faru ba, muna gidan Sarki dukkanin mu jami'an Gwamnati. Me zaku ce?
Cikin Lumana Muka Yi Zaɓen 2019 Amma Aka Ƙirƙiro Mana Inkwankulusib, Céwar Ja’afar Ja’afar

Cikin Lumana Muka Yi Zaɓen 2019 Amma Aka Ƙirƙiro Mana Inkwankulusib, Céwar Ja’afar Ja’afar

Duk Labarai, Kano
Lafiya ƙalau mu ka yi zaɓen farko a Kano a 2019, amma su ka ƙirƙiri fitinar ‘inconclusive’, suka kawo ‘yan ďàbà suka raunana mutane suka kwace zaɓen. Lafiya ƙalau majalisa ta yi dokar cire sarakuna babu tarzoma, kowa ya koma sha’aninsa, amma daga baya su ka kawo sojoji da 'yan ďaba suna tada husuma a gari. Allah Ka yi mana maganin duk wanda ke da hannu a haɗa wannan fitina.
Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Masoya tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun yi Sallah inda suka roki Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano. Ranar Alhamis ne dai majalisar Kano ta soke dokar data kirkiro masarautu 4 a Kano sannan ta sauke Aminu Ado Bayero inda aka dawo da tsohon Sarki, Muhammad Sanusi II kan karagar Sarautar. Saidai Aminu Ado ya koma Kano inda ya je gidan Nasarawa ya kafa fadarsa acan, kuma masoyansa sun mai maraba. An ga masoyan Tsohon sarkin da yawa suna Sallah inda suke rokon Allah ya dawo dashi kan karagar sarautar Kano.