Alamomin cikin wata tara
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum.
A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm
Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai.
Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa.
Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari.
Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi.
Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu.
Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.