Addu’a ga mai ciki: Addu’ar saukin haihuwa
Wannan addu'a da zamu baku anan manyan malamai sunce sadidan ce, an gwada akan mata dake nakuda kuma an yi nasara:
Saidai kamin mu baku wannan addu'a, ga bayani kamar haka:
A binciken masana malamai na sunnah sun ce babu wata addu'a da aka ware wadda aka ce mace me ciki zata rika yi.
Malamai sunce akwai dai hadisan karya da ake dangantawa da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) akan addu'a ga mai ciki.
Misali Akwai hadisin da aka ce, A lokacin da fatima(A.S) ta zo haihuwa, Ma'aikin Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yasa Umm Salamah da Zaynab bint Jahsh su zo su karanta mata Ayatul Kursiyyu, da kuma al-A‘raaf 7:54, Yoonus 10:3, da kuma falaki da Nasi, Saidai wannan hadisin karyane, domin karin bayani ana iya duba al-Kalim at-Tayyib (p. 161) na Ibn Taymiy...