Alamun ciki yakai haihuwa
Akwai alamu da yada dake nuna ciki ya jai haihuwa:
Zaki iya jin zafi sosai kamar na lokacin al'ada.
Zaki ji mahaifar ta matse sannan zata saki.
Hakan zai iya ci gaba da faruwa, yana zuwa yana tafiya duk bayan mintuna 5, kuma lokaci na tafiya hakan na kara tsananta.
Da kinji haka to a kira ungozoma ko kuma a kaiki asibiti, Haihuwa ta zo.
Zaki iya jin ciwon baya sosai.
A yayin da kike da ciki, wani ruwa me yauki yana taruwa ya kulle kofar mahaifarki, to a yayin da kika zo haihuwa, wannan ruwan zai fito waje, idan kika ganshi, me yauki ne kuma Pink to haihuwa ta zo, saidai wasu na haihuwa ba tare da ganin ruwan ba.
Amma masana kiwon lafiya sun ce rashin ganin ruwan ka iya zama alamar cewa akwai matsala tare da ke ko abinda zaki haifa. Dan haka ya kamata a nemi ungozoma ko...