Kanunfari yana maganin sanyi
Tabbas Kanunfari yana maganin sanyi kamar yanda masana ilimin kiwon lafiya suka tabbatar.
A mafi yawancin lokuta akan hada Kanunfari da zuma ne dan samun sakamakon maganin sanyi me kyau.
Masana sun bayyana hadin Kanunfari da zuma a matsayin na gaba-gaba wajan magance matsalar sanyi da mura.
A yayin da mutum ke fama da kaikayin makogoro, shima wannan hadi na da tasirin da zai magance wannan matsalar.
Yanda ake hadin shine:
Za'a samu Kanunfari kamar kwaya 6 a dan dorasu a wuta a dan gasa.
Sannan a daka su su zama gari.
Sai a zuba babban cokali na zuma a ciki.
Ana shan wannan hadi sau biyu zuwa uku a kullun dan maganin tari mura da kaikayin makogoro.