fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Jihar Zamfara za ta dauki kwararrun ma’aikatan lafiya 515 domin inganta kiwon lafiya

Gwamnatin Jihar Zamfara za ta dauki kwararrun ma’aikatan lafiya 515 domin inganta kiwon lafiya

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Zamfara ta ce za ta dauki ma’aikata 515 na asibiti a matsayin wani mataki na dinke barakar da ke damun ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya na sakandare a jihar. Dr Bashir Maru, Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Asibitin Jihar Zamfara ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Juma’a a Gusau, babban birnin jihar. Maru ya ce Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya umurci hukumar kula da ayyukan asibitocin jihar da ta gudanar da aikin daukar ma’aikata. Ya ce daukar ma’aikatan wani bangare ne na kudirin gwamnatin na karfafa tsarin kiwon lafiya a jihar.
Babbar magana: Ma’aikatan lafiya 900 za su iya rasa aikin su a birnin tarayya, Abuja

Babbar magana: Ma’aikatan lafiya 900 za su iya rasa aikin su a birnin tarayya, Abuja

Kiwon Lafiya
Kimanin ma'aikatan lafiya 900 a babban birnin tarayya (FCT) ne ake tunanin za su iya rasa ayyukansu. Hakan ya faru ne saboda hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja (FCTA), ta baiwa manajojin asibitin Garki wa’adin wata guda da su bar wurin. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan mataki da gwamnatin ta dauka ya biyo bayan karewar yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP) tsakanin Firimiyan hukumar ta NISA- manajojin asibitin Garki na yanzu da na FCTA. An rattaba hannu kan yarjejeniyar rangwame ga PPP tsakanin Firayim Ministan NISA da FCTA a cikin 2007 na tsawon shekaru 15. The Nation ta rawaito cewa sama da ma’aikata 900, da suka hada da masu ba da shawara 21, likitocin kiwon lafiya 113, jami’an gidaje 24, ma’aikatan jinya 159, ma’aikatan j...
Daduduminsa: Masana kimiyyan Najeriya sun gano magungunan cutar zazzabin Lassa

Daduduminsa: Masana kimiyyan Najeriya sun gano magungunan cutar zazzabin Lassa

Kiwon Lafiya
Masana kimiyya na hukumar NABDA sun gano magunguna wanda za ayi amfani dasu domin magance cutar zazzabin Lassa. Farfesa Abdullah Mustapha, wanda ya kasance darekta a NABDA ne ya bayyana hakan yayin da yake fira da manem labarai ranar juma'a a Abuja. Inda ya bayyana cewa sun gano wa'yan nan magungunan ne domin taimakawa Najeriya a kawo karshen cutar zazzabin Lassa.  
Gwamna Mai Mala Buni ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 196 aiki a Jihar Yobe

Gwamna Mai Mala Buni ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 196 aiki a Jihar Yobe

Kiwon Lafiya
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da daukar ma’aikata kai tsaye ga dalibai 196 da suka kammala karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Nguru. Buni, a wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da hulda da manema labarai Alhaji Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu, ya ce samar da ayyukan yi ga jami'an lafiyar zai bunkasa fannin kiwon lafiya. Ya kara da cewa ma’aikatan sun hada da kwararrun likitocin harhada magunguna 23, kwararrun dakin gwaje-gwaje na likitanci 60, kwararrun likitocin aikin tiyatar hakori 62 da kwararrun kula da bayanan lafiya 51.
An dasa wa wani mutum zuciyar alade a Amurka

An dasa wa wani mutum zuciyar alade a Amurka

Kiwon Lafiya, Uncategorized
Likitoci a Amurka sun yi nasarar dasa wa wani mutum zuciyar alade, a irin wannan aiki da ke zaman na farko a duniya, inda mutumin yake murmurewa kwana uku bayan dashen. Likitoci sun bayyana aikin da cewa gagarumin ci gaba ne da kuma nasara, domin ana ganin a karshe zai kai ga ana amfani da hanyar wajen yin amfani da sassan dabbobi domin yi wa mutane dashe. Likitocin da suka jarraba wannan sa'a a asibitin Jami'ar Maryland sun ce zuciyar aladen wadda aka yi wa kwaskwarima ta yadda jikin dan adam zai iya karbarta, tana aiki a jikin mutumin kalau, bayan aikin na tsawon sama da sa'a bakwai. Rahotanni sun baiyana cewa likitocin sun kuma ce zuwa wasu sa'o'i 24 za a iya cire wata na'urar da aka hada wa mutumin da aka yi wa aikin David Bennett, mai shekara 57, da ke taimaka masa. Ai...
Shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a>>NAFDAC

Shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a>>NAFDAC

Kiwon Lafiya
Hukumar tsabtace Sahihancin Magunguna da Abinci ta Ƙasa, NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju'a, ma'ana, mutuwar gaggawa. Hukumar ta ƙara da cewa magungunan karfin maza kan haifar da cutar ɓarin jiki inda maza za su riƙa shan su domin su burge matan da su ke saduwa da su. Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a saƙon ta na Kirsimeti da sabuwar shekara. Adeyeye ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan. A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin. "Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya. Inda su na da rijista, to masu shigo da shi da masu sayarwa ba za su riƙa yin abin da su ke yi a kasuwanni, ka tuna, kafafen sad...
Dawowar Coronavirus Da Duminsa: Gwamnatin tarayya tace daga yau yawan mutanen da zasu shiga masallaci kada ya wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai dauka

Dawowar Coronavirus Da Duminsa: Gwamnatin tarayya tace daga yau yawan mutanen da zasu shiga masallaci kada ya wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai dauka

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta dawo da dokar kayyade yawan mutanen da zasu shiga masallaci saboda dawowar annobar Coronavirus gadan-gadan.   Gwamnatin tace duka wajan ibada na Najeriya,  mutanen da zasu shiga ciki, kada su wuce kaso 50 cikin 100 na yawan mutanen da wajan ibadar zai dauka.   Shugaban kwamitin dake kula da yaduwar cutar coronavirus,  Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.   Yacw idan cutar ta ci gaba da yawaita, dole su saka karin dokoki masu tsauri.
Mun aikawa Kano Biliyan 5 ta yaki coronavirus>>Gwamnatin Tarayya

Mun aikawa Kano Biliyan 5 ta yaki coronavirus>>Gwamnatin Tarayya

Kiwon Lafiya
Kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da yaki da cutar coronavirus ya bayyana cewa an sake aikawa jihohi kudade dan su yaki cutar coronavirus.   Shugaban kwamitin, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai.   Yace an aikawa jihar Legas Biliyan 10 inda aka aikawa Kano Biliyan 5 sannan kuma an aikawa sauran jihohin Najeriya Biliyan 1 kowacce su yaki coronavirus.
Za’a Kwashe Shekaru 120 Kafin A Sami Wadatar Likitocin Da Ake Nema A Najeriya>>Ministan Ilimi

Za’a Kwashe Shekaru 120 Kafin A Sami Wadatar Likitocin Da Ake Nema A Najeriya>>Ministan Ilimi

Kiwon Lafiya
Minista Adamu Adamu ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsuwar fara karatun digiri karo na farko na jami’ar kimiyyar kiwon lafiya ta tarayya wato FUHSO, da aka gudanar a mazaunin jami’ar na wuccin gadi dake garin Otada na karamar hukumar Otukpo a jihar Binuwai. Adamu ya ce jami’ar ta FUHSO da ke jihar Binuwai za ta cike gibin da ake samu na bukatar likitoci a Najeriya. Ministan wanda ya sami wakilcin babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Sunny Echono, ya ce idan aka yi la'akari da adadin likitocin da ake yayewa a Najeriya a halin yanzu, kasar za ta kwashe kimanin shekaru 120 kafin ta samu adadin likitocin da take bukata a fannin kiwon lafiyarta, amma kuma sai idan likitocin da ke aiki a kasar sun ci gaba da aiki ba tare da fita kasashen waje aiki ba. Haka kuma, Adamu...