Monday, December 9
Shadow

Tafarnuwa na maganin sanyi

Tafarnuwa na daya daga cikin abubuwan da aka dade ana amfani dasu wajan maganin gargajiya shekaru da yawa da suka shide a Duniya.

Misali ana amfani da tafarnuwa wajan magance matsalar Ciwon zuciya, kara karfin tunani da magance ciwon mantuwa, tana karawa garkuwan jiki inganci, tana bayar da garkuwa ga cutar daji watau Cancer kala-kala.

Amma a wannan rubutu, zamu yi maganane akan yanda ake amfani da Tafarnuwa wajan magance matsalar sanyi.

Domin Maganin Sanyi ana tattauna Tafarnuwa ko a daddakata a rika sha.

Hakanan bincike ya bayyana cewa, Cin Tafarnuwa yana baiwa mutum garkuwa daga kamuwa da ciwon sanyi da mura.

Hakanan ko da mutum ya kamu da murar idan dai yana cin tafarnuwa kullun to murar ba zata dade ba zata warke, kamar yanda masana suka sanar.

Karanta Wannan  Amfanin man zaitun da tafarnuwa

Masana sun ce ana son a daddaka tafarnuwa kamin a ci ta.

Hakanan tafarnuwa wadda ta dade a ajiye kamar shekara daya da rabi tafi yin maganin sanyi da mura.

Hakanan akan so mutum ya ci ta guda 3 zuwa hudu a rana.

Allah ya kara lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *