Alamomin mace mai sha’awa
Kowace mace na da sha'awa saidai sha'awa karfi-karfi ce akwai wadda sha'awarta na da karfi akwai wadda sha'awarta bata da karfi.
Cima watau abinci na da tasiri sosai wajan sha'awa ga dukkan jinsin namiji da mace. Macen da take cin abinci me gina jiki sosai zata fi samun sha'awa akai-akai fiye da wadda bata cin abinci me gina jiki ko take cin garau-garau.
Hakanan Kwanciyar hankali na daya daga cikin abubuwan dake da tasiri a yanayin sha'awar mutum, macen dake samun kwanciyar hankali bata yawan yin aikin wahala takan samu sha'awa fiye da wadda ke aikin wahala sosai.
Yawanci ana alakanta sha'awar mace da:
Jan Ido.
Yawan Kallo.
Son jiki.
Shiru-shiru.
Dadai sauransu.
Kamar dai yanda muka bayyana a sama, kowace mace da yanayin karfin sha'awarta.