Kasar Maldives ta haramtawa Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan Falasdinawa
Kasar Maldives ta zama ta farko data hana mutanen kasar Israela shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa.
Yakin da kasar Israela take yi da Falasdinawa dai ya fara jawo mata Allah wadai har ma daga manyan kasashe.
Kasa ta baya-bayannan data dauki mataki akan kasar Israela itace kasar Faransa wadda ta hana kasar ta Israela halartar taron bajakolin makamai mafi girma a Duniya.