Saturday, July 13
Shadow

Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Dan majalisar kasar Faransa, Sébastien Delogu ya daga tutar Falas-dinawa a farfajiyar majalisar yayin da ake zaman zauren majalisar.

Dan majalisar yace kasarsa ta Faransa na da hannu a kisan kare dangin da Israela kewa Falas-dinawa ta hanyar sayarwa da Israelan makamai.

Yayi kira ga shugaban kasar, Emmanuel Macron da ya daina sayarwa da Israela makamai.

Saidai an dakatar dashi sannan aka bashi dakatarwar kwanaki 15.

Karanta Wannan  Firaministan Israela, Benjamin Netanyahu yace harin da sojojin kasarsa suka kai a Rafah kuskurene

Saidai bayan dakatar dashi, Dan majalisar ya shiga cikin masu zanga-zangar goyon bayan kasar ta Falas-dinawa a kan titi:

Saidai a wani lamari kuma na ban mamaki, shine, kakakin majalisar data dakatar dashi, itama an ganta sanye da tutar kasar Israela yayin da take wani jawabi.

Wannan yasa aka rika bayyana lamarin da son kai da munafurci.

Karanta Wannan  Hotuna da Bidiyo:Zanga-zanga ta barke a kasar Mexico inda 'yan kasar suka fito suna goyon bayan Falasdinawa, sun yi yunkurin kona ofishin jakadancin kasar Israela

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *