Thursday, June 5
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: EFCC ta kama Aisha Achimugu a filin jirgin sama na Abuja

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, sun kama ƴar bokon nan kuma ƴar kasuwa, Aisha Sulaiman Achimugu.

Lauyan Achimugu, Chikaosolu Ojukwu ne ya shaida wa Nairametrics a wani sako da ya aike a safiyar yau Talata.

Ya ce an kama Achimugu daga saukar ta daga jirgi bayan ta dawo daga London da misalin ƙarfe 5 na asuba.

Tun a baya, lauyan Achimugu ya baiyana wa babbar kotun tarayya a Abuja cewa a yau wacce ya ke karewa za ta kai kan ta ga EFCC a binciken zargin da ake mata na karkatar da wasu kuɗaɗe.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Yanda sojojin Najariya suka kafa tutar Najeriya bayan kwace iko da maboyar 'yan Bìndìgà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *