
Gungun Malaman Firamare da sauran ma’aikatan ƙananan hukumomin Abuja sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan tituna, kan rashin biyan su mafi ƙarancin albashi, da sauran haƙƙoƙin da suke bin shugabannin ƙananan hukumomi 6 da ke Abuja.
Sun gudanar da zanga-zangar ne a yau Alhamis a ƙarƙashin ƙungiyar malaman makaranta ta NUT, da kuma ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta NULGE.