Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce nan ba da dadewa ba zai aika da sabuwar dokar mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar dimokradiyya a ranar Laraba.
Ya ce gwamnatinsa ba ta murkushe kungiyar kwadago ba kamar yadda gwamnatin kama-karya ta yi.
“Mun yi shawarwari cikin nasara kuma mun yi tattaunawa tare da kungiyoyin kwadago a kan mafi karancin albashi na kasa, nan ba da jimawa ba za mu aika da kudirin zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa domin tabbatar da abin da aka amince da shi a cikin shekaru biyar masu zuwa ko kasa da haka,” in ji shi.
Ku tuna cewa kwamitin mafi karancin albashi na kasa ya mika rahotonsa ga shugaban kasa a ranar Litinin.
A cikin rahoton, gwamnatin tarayya ta gabatar da shawarar mafi karancin albashi na N62,000 sannan kungiyar kwadago ta nemi N250,000.
Haka kuma, Gwamnoni da kamfanoni masu zaman kansu sun bayar da shawarar N57,000 da N62,000.
Daga: Abbas Yakubu Yaura