Gwamnatin tarayya ta sanar da kudirinta na son tura dan Najeriya na farko zuwa Duniyar wata.
Shagaban hukumar kula da sararin Samaniya ta Najeriya, Mathew Adepoju ne ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja.
Ya bayyana cewa tuni Nigeria ta kulla yarjejeniya dan cimma wannan matsayi.
Ya bayyana cewa, Wannan ba karamin ci gaba zai kawowa Najeriya ba ta fannin bincike da kimiyya a sararin samaniya.