
Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa ta shirya tsaf dan gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna.
Hukumar tace za’a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne bisa zargin Almundahanar kudade, damfara da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba.
Sanarwar tace za’a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne tare da wani me suna Joel Adoga ranar 24 ga watan Maris.
Hakanan sanarwar tace akwai shari’a ta daban itama da za’a shigar da tsohon gwamnan Kadunan a babbar kotun jihar kaduna itama inda ake zarginsa da aikata ba daidai ba da ofishinsa da kuma karkatar da kudade.