Saturday, June 27
Shadow

Da Duminsa: A karshe dai ICPC ta saka ranar da zata Gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban kotun Gwamnatin tarayya

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa ta shirya tsaf dan gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna.

Hukumar tace za’a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne bisa zargin Almundahanar kudade, damfara da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba.

Sanarwar tace za’a gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne tare da wani me suna  Joel Adoga ranar 24 ga watan Maris.

Hakanan sanarwar tace akwai shari’a ta daban itama da za’a shigar da tsohon gwamnan Kadunan a babbar kotun jihar kaduna itama inda ake zarginsa da aikata ba daidai ba da ofishinsa da kuma karkatar da kudade.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Mukan Shiga kasa mu yi Yaqi ba wai dan mu yi nasara ba, Kawai mukan jefa BoumaBoumai mu daidata rayuwar mutanen kasar mu kara gaba>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *