Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Allah Sarki, Sojannnan Muhammad dake ta neman a bashi damar ya ajiye aiki aka ki bashi dama har ya fito yayi Bidiyo ya gayawa Duniya, an kamashi an daure a Guard Room

Rahotannin da muke samu na cewa, sojan Najeriya, Muhammad da ya fito ya gayawa Duniya cewa, yana ta so ya ajiye aiki amma na sama dashi sun ki bashi dama, an kamashi an daureshi a Guard Room.

Wani na kusa dashi me sunan Mustapha Muhammad ne ya bayyana hakan inda yace matar sojan ke gaya masa halin da mijinta ke ciki.

Sojan dai ya bayyana cewa wata matsalar iyali ce tasa yake son ajiye aikin nasa inda yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Ministan tsaro da shuwagabannin soji da majalisar tarayya su taimaka masa kan maganar ajiye aikin.

Karanta Wannan  Wani Kamfanin mai daga kasar waje ya zo kusa dani ya kama hayar matatar man fetur dan ya rika tace man fetur da bashi da inganci>>Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *