
Rahotanni sun bayyana cewa yawan sojojin da ake tsare dasu ana bincikensu kan zargin hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki sun kai 42.
A baya dai rahotanni sun ce sojoji 16 ne aka kama ake bincike.
Saidai a yanzu yawan sojojin sun kai 42 wanda ake bincike kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jaridar tace wasu majiyoyi a gidan sojin sun sanar da ita cewa, ana gayyatar manyan sojoji inda ake musu tambayoyi game da zargin hannu a yunkirin juyin mulkin.