Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Bayan da yace bai yadda a bincikeshi ba kan Gwamnan rikon kwarya na watanni 6 da yayi a jihar Rivers ba, Ibas ya gana da shugaba Tinubu, da shugaban EFCC da Ministan Kudi a daren jiya

Gwamnan rikon Kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas wanda ya shafe watanni 6 a mukamin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadarsa dake Abuja da yammacin jiya, Laraba.

Rahotanni daga Punchng sun ce ganawar ta samu halartar Ministan kudi, Wale Edun da kuma shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode.

Saidai ba’a samu bayani kan abinda suka tattauna ba.

Hakan na zuwanw kwanaki 3 bayan da Ibas yace bai yadda da shirin binciken da majalisar jihar Rivers ke shirin yi masa ba inda yace Bincikensa kamar binciken shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne da majalisar tarayya domin shi Tinubu ne ya bashi aiki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ina da Karama, Kuma ina gaya muku ko dai a taso a taimaka mana wajan kokarin kawo zaman lafiya da muke a Arewa ko kuma abinda za'a gani nan gaba sai yafi abinda ake ciki yanzu>>Inji Sheikh Musa Asadussunnah

Rahotanni sun ce Jihar Rivers me arzikin mai ta samu makudan kudaden shiga da suka Haura daruruwan Biliyoyin Naira a watanni 6 da Ibas yayi na gwamnan rikon kwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *