Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Jami’ar da aka ce ta baiwa Rarara Digirin girmamawa tace damfarar Mawakin aka yi, bata san da maganar ba

Rahotanni sun ce jami’ar The European-American University da aka ce ta baiwa Dauda Kahutu Rarara Digirin girmamawa na Dr. Tace bata san da maganar ba.

Jami’ar tace wadanda suka ce su wakilanta ne har suka baiwa Dauda Kahutu Rarara Digirin karya suke ba wakilanta bane.

Kafar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a sanarwar da jami’ar ta fitar tace zata kai wadanda sukawa Rarara wannan Damfara kotu dan a hukuntasu.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya Ta Tara Naira Bilyan 60 Daga Cire Tallafin Taki, Inji Hukumar NSIA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *