Tuesday, May 5
Shadow

Da Duminsa: Ji Wani Tuggu da ake shiryawa dan hana Farfesa Isa Ali Pantami takarar Gwamna a jihar Gombe

RIGIMA TA ƁARKE A APC A GOMBE, ZA A HANA PANTAMI TAKARAKA.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bukaci tsohon Ministan Sadarwa, Prof. Isa Ali Pantami, da ya janye burinsa na takarar gwamna tare da mara wa ɗan takarar da jam’iyyar APC za ta tsayar baya.

An ce wannan ya faru ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a daren yau a Gidan Gwamnatin jihar Gombe.

Majiyoyi sun bayyana cewa Pantami bai ji daɗin wannan shawara ba, lamarin da ka iya haifar da sabani a cikin jam’iyyar.

Me kuke ganin zai biyo baya a siyasar Gombe?

Daga DDLHausa

Karanta Wannan  MAAN ta nemi taimakon EFCC, DSS da ƴansanda wajen karɓo bashin da manoman masara su ka karba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *