
Rikici ya ɓarke a taron masu ruwa da tsaki na APC a mazaɓar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado a Kano
Rahotanni na baiyana cewa rikicin ya ɓarke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano a yankin mazaɓar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado.
Wata jaridar yanar gizo, Arewa Updates ta rawaito cewa rikicin ya fara ne bayan da Hajiya Hasiya Aminu, shugabar mata ta jam’iyyar NNPP ta Dawakin-Tofa waɗanda suka koma APC, ta ƙalubalanci ɗan majalisar tarayya na yankin, Tijjani Abdulkadir Jobe, wanda tare da shi suka koma NNPP a can baya.
Jaridar ta rawaito cewa Hajiya Hasiya ta ƙalubalanci Jobe wajen gazawa ta kulawa da ƴan jam’iyya, har take kiran da ya yi koyi da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Anas Mukhtar Bello DanMaliki da kuma Engr. Abba Ganduje, abin da ya hasala ɗan majalisar tarayyan.
Rahotonni sun nuna cewa, tana tsaka da jawabin ne sai dan majalisar ya yi zumbur, ya ce sai ya bata amsa, amma sai aka yi kokarin hana shi, har ma aka kwace lasifika.
A nan ne waje ya kaure, inda aka kekketa rigar mai gabatar da taron wato MC wanda ya sha da ƙyar, bayan da wasu fusatattun matasa masu goyon bayan dan majalisar su ka tarwatsa taron.
Wani daga mahalarta taron ya shaida wa Arewa Updates cewa masu ruwa da tsakin jamʼiyyar da dama sun kai da ƙafarsu.
Wannan dai shi ne taro na farko da ya haɗa tsagin Dan Majalisa Joɓe da kuma na Engr. Abba Ganduje wanda suka kara a zaɓen 2023 kuma ba sa ga maciji da juna.
Haka zalika wannan shine karo na farko da ya haɗa ƴan siyasar yankin da ke bangarorin Kwankwasiyya da Gandujiyya a inuwa ɗaya.
Daga cikin mahalarta taron sun hada da masu neman takarar kujerar majalisar tarayya ta yankin, Barr. Munir Dahiru Maigari, Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Rimingado da Dr. Jinaidu Yakubu Tofa, Engr. Abba Ganduje, sai kuma Babban Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ya halarci taron ta wayar tarho.
Sauran jagororin jamʼiyyar da suka halarta sun haɗa da Malam Sani Tofa Mai Ba Gwamna Shawara kan ayyuka na musamman, kuma tsohon shugaban hukumar shariʼa ta Kano.
Tsofaffin Kwamishinonin Ayyuka na Kano Engr. Hamisu Lambu, Shehu Haruna Lambu, da Idris Garba Unguwar Rimi.
Tsohon Kwamishinan Kasa na Kano Muhammad Nadu Yahaya, Farfesa Nura Yaro Dawakin Tofa, Farfesa Kabiru Dungurawa, Tsohon Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano, sai Ibrahim Umar tsohon kantoman Tofa, sai Muhammad Bello Butu-butu, Mataimakin Shugaban Majlaisar Dokokin Kano, Barr Muhyi Magaji Rimingado, Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano, Ahmad Muhammad Speaker Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa da sauran su.