
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bayar da Belin tsohon Ministan shari’a, Abubakar malami inda yake neman a sakeshi daga komar EFCC.
Saidai kotu a zamanta na ranar Alhamis tace EFCC ta ci gaba da tsare Malami inda Mai Shari’a, Babangida Hassan yace ci gaba da tsare Abubakar Malami bai sabawa doka ba.