
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana shirinta na yin zanga-zanga ranar 17 ga watan Disamba saboda matasalar tsaro.
kungiyar ta bayyana hakane a wata sanarwa data fitar ranar 10 ga watan Disamba bayan wani taro data yi.
Ta yi magana musamman akan satar daliban makaranta na jihar Kebbi.
Ta yi kiran Gwamnati ta dauki matakin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.