Saturday, December 13
Shadow

Da Duminsa: Matatar Man fetur din Dangote ta rage farashin man

A wani yanayi da zai iya kawo sauki ga matsin rayuwa musamman ga talakawan Najeriya, Matatar man Dangote ta rage farashin litar mai da ake dauka a Depot daga Naira 950 zuwa Naira 890 akan kowace lita.

Matatar man ta ce ta rage kudinne saboda saukar farashin danyen man fetur a Kasuwar Duniya.

Me magana da yawun matatar man fetur din, Anthony Chiejina ne ya bayyana haka inda yace kamar yanda a ranar 19 ga watan Janairu da ya gabata suka kara farashin litar man fetur din saboda tashin farashin danyen man fetur din hakanan a yanzu tunda farashi ya sauka shine suma suka rage farashin.

Karanta Wannan  Makarantar Horas da sojoji ta Najeriya, NDA zata bude damar neman aikin soja daga gobe

Matatar tace wannan rage farashin zai kawo saukin hauhawar farashin kayan masarufi da saukin rayuwa a tsakanin ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *