
A wani yanayi da zai iya kawo sauki ga matsin rayuwa musamman ga talakawan Najeriya, Matatar man Dangote ta rage farashin litar mai da ake dauka a Depot daga Naira 950 zuwa Naira 890 akan kowace lita.
Matatar man ta ce ta rage kudinne saboda saukar farashin danyen man fetur a Kasuwar Duniya.
Me magana da yawun matatar man fetur din, Anthony Chiejina ne ya bayyana haka inda yace kamar yanda a ranar 19 ga watan Janairu da ya gabata suka kara farashin litar man fetur din saboda tashin farashin danyen man fetur din hakanan a yanzu tunda farashi ya sauka shine suma suka rage farashin.
Matatar tace wannan rage farashin zai kawo saukin hauhawar farashin kayan masarufi da saukin rayuwa a tsakanin ‘yan Najeriya.