
Abunda Gwamna Zulum yake yi wa talakawan jihar sa na rushe gidajen su sam bai dace ba koda kuwa local dillalai ne suka cuce su na saida musu filayen da bana su ba.
Na tabbata akwai wadanda da yawa ba su da masaniyar yadda abun yake kuma hakan zai iya zama silar talaucewar mutane da yawa.
Ya kamata Gwamnatin jihar ta kama dukkannin dillalan da suka cuci al’umma domin su biya wa ‘yanda suka saidawa wurin hakkokinsu, haka zalika Gwamna Zulum shima ya ragewa wa ‘yanda hakan ya shafa asara ta hanyoyi da dama.
Daga Comr Abba Sani Pantami